Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta kama mutane hudu da ake zargi da fashi da makami tare da kwato wasu kayayyaki da aka sace bayan wani fashi da makami da aka yi kwanan nan a babban birnin jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Ahmed Wakil ya fitar a ranar Laraba.
- Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista
- An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano
Sanarwar ta ce, “A ranar 11 ga Nuwamba 2025, rundunar ta sami koke daga wani Everest Jonathan na ofishin V.I.O da ke kan titin Jos, Bauchi, a hedikwatar ‘yansanda ‘B’, wanda ke nuna cewa, wasu ‘yan fashi da makami da suka kai kimanin biyar sun mamaye gidansa sun yi masa fashi, inda suka yi awon gaba da kayayyakinsa masu daraja.
Wakil ya ce, bayan samun rahoton, tawagar ‘yansanda karkashin jagorancin jami’in ‘yansanda na sashin, CSP Holman Simon, sun ziyarci wurin nan take domin tantance irin barnar da aka yi.
Ya bayyana cewa, binciken farko ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Alhassan Jibrin, wanda aka fi sani da Babani Biri, matashi mai shekaru 20 mazaunin yankin Danjuma Goje, Bauchi, ya jefar da wayarsa ta Android a wurin da aka yi fashin.
“Binciken ya kai ga kama wasu mutane uku: Lawan Adamu, da Lawan Idris, mai shekaru 20, da Muhammad Yau, wanda aka fi sani da Madugu, mai shekaru 22, duk mazauna Bauchi ne” in ji CPRO














