Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi kira ga kasar Japan da ta janye kalaman baya-bayan nan da firaministar kasar ta furta, dangane da yankin Taiwan na kasar Sin, in ba haka ba, ta shirya girbar sakamakon danyen aikinta.
Lin Jian, ya yi kiran ne yayin taron ganawa da manema labarai na yau da kullum a yau Alhamis, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa dangane da kalaman firaministar Japan Sanaen Takaichi, game da yankin Taiwan na kasar Sin, wadanda kuma ta ki ta janyewa.
Lin, ya ce a baya-bayan nan Takaichi ta furta kalaman tayar da husuma, dangane da yankin na Taiwan, yayin da take tsokaci a majalisar dokokin kasarta, inda ta ambata yiwuwar aiwatar da matakan soji a zirin Taiwan. Lin ya ce kalaman na firaministar Japan ba su dace ba, sun kuma yi matukar keta manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da ruhin takardun siyasa hudu, wadanda Sin da Japan suka daddale, da ma yanayin gudanar da alakar kasa da kasa.
Jami’in ya kara da cewa, wadannan kalamai na firaministar Japan, matukar tsoka baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, sun kuma kalubalanci moriyar kasar, tare da keta hurumin ‘yancin kan kasar ta Sin. Don haka Sin ke matukar adawa da su, kuma ba za ta amince da hakan ba. (Saminu Alhassan)













