Kungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta yi gargadi cewa yanayin da tattalin arzikin da kasar nan ke ciki ya jefa kafofin yada labarai cikin wani mawuyacin hali.
Kungiyar ta kuma yi kira da a soke dokokin da ke takura ‘yancin ‘yan jarida. Shugaban NGE, Mista Eze Anaba, ya bayyana haka ne a jawabin maraba da ya yi a Taron Editocin Nijeriya Gabadaya (ANEC) mai taken “Dimokuradiyya, Gudanarwa da Hadin Kan Kasa: Rawar da Editoci ke Takawa,” wanda aka gudanar a dakin taro na Tarayya, Abuja.
Ya yi nanata cewa halin tattalin arziki a kasar ya tilasta wasu gidajen jarida rufewa, yayin da wasu da ke kokarin ci gaba da aiki ba sa iya biyan albashin ma’aikata.
A cewarsa, wannan lamari ne ke kara yawan rashin aikin yi, domin yana tura ma’aikatan wadannan gidajen jarida zuwa wasu ayyuka na leburanci. Ya nemi tallafi daga bangaren dokoki da na gudanarwa domin tabbatar da dorewar kafofin yada labarai, tare da sassauci kan harajin kamfanoni na tsawon kusan shekaru goma.
The NGE boss also called for tad edemption, the establishment of low-interest loans for the media, and a digital transformation and innobation fund.
Anaba further proposed a Media Freedom and Safety Charter to protect journalists from the hostile enbironment.
Shugaban NGE ya kuma yi kira da a ba da ‘yancin rage haraji, kafa lamuni mai riba kasa ga kafofin yada labarai, da kuma kafa asusun canjin zamani da kirkira na dijital.
Anaba ya kuma ba da shawarar kafa Charter na ‘Yancin ‘Yan Jarida da Tsaronsu domin kare ‘yan jarida daga mawuyacin yanayi.














