ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

by Sani Anwar
3 hours ago
Amurka

Kafin Nijeriya ta samu cikakken zaman lafiya da tsaro a fadin Arewa da kuma kudancin kasar, dole ne kowa da kowa ya ba da tasa gudunwara.

Wannan ne ra’ayin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da kuma tsohon Shugaban Hafsan Sojoji, Abubakar Danbazau, sun bayyana wannan ra’ayi nasu ne a ranar Litini da ta gabata, a wajen taron koli na dandalin tattaunawa da harkar tsaro, karo na farko da Gwamnatin Jihar Kebbi tare da hadin gwiwar ‘Arewa Broadcast Media Practitioners Forum’ (ABMPF), suka shirya a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Birnin Kebbi.

  • Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
  • Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe

Sultan Sa’ad, ya bayyana taron a matsayin wanda aka shirya a daidai lokacin da ya dace, kuma ‘yan wannan kasa za su fahimci gaskiya da sanin inda aka sanya gaba, a cewarsa; al’ummar kasar nan na fuskantar hare-hare da kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane.

ADVERTISEMENT

“Wannan wani taro ne da za a tattauna batutuwan da suka shafi rashin tsaro bayan taron da muka gudanar kwanan nan a taron masu rike da sarautun gargajiya da aka yi a Kebbi,” in ji shi.

Ya ce, za su dauki matakin kawar da duk wani nau’in ‘yan fashi da sauran miyagun ayyuka a Arewacin Najeriya.

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici.

Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta bari wasu kasashe su raba kawunansu, ya kuma bayar da tabbacin cewa; duk da kalubalen da ake fuskanta, Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa mai girma da kuma ci gaba da samun hadin kai.

Har ila yau, Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Abubakar Danbazau, a jawabinsa ya bayar da shawarar cewa; dole ne a magance matsalar rashin tsaro, matsalolin fatara, sauyin yanayi, rashin aikin yi da kuma amfani da kudaden tarayya da aka kayyade.

A cewarsa, kwararar masu tsattsauran ra’ayin addini cikin kasar, ya taimaka wajen tabarbarewar tsaro da ke bukatar daukar matakin yaki da su ko kuma korar su daga kasar baki-daya.

Kazalika, ya kuma bukaci Gwamnonin Arewa da su yi amfani da kudaden asusun tarayya, ta hanyar samar da guraben ayyukan yi da samar da karin masana’antu, domin samun ci gaban tattalin arziki.

A cewar tasa, alkaluma sun nuna cewa; sakamakon ayyukan ‘yan fashi da makami, ya hana kimanin yara miliyan 10 shiga makarantun firamare da sakandare a Arewacin Najeriya.

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, a wani faifan bidiyo da ya gabatar a wurin taron, ya yaba wa wadanda suka shirya taron, musamman ganin cewa; an riga an tattauna batun rashin tsaro a taron Kungiyar Gwamnonin Arewa.

“An yi matukar samun nasarori a wannan taro, kana kuma an tura jami’an tsaro ko’ina a Arewacin kasar nan,” in ji shi.

Gwamna Uzodimma Ya Bukaci Sarakunan Gargajiya Su Jagoranci Yi Wa Kasa Adduo’I’n Zaman Lafiya

Biyo bayan matsin lamba da ake yi wa Nijeriya, kan kashe-kashen da rashin tsaro ke haifarwa, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Cif Hope Uzodimma, ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da su rika yin addu’o’i, domin samun saukin matsalar tsaro.

Uzodimma, wanda shi ne Gwamnan Jihar Imo, ya jagoranci sauran gwamnonin wajen kai wa Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Neja ziyara, domin jajanta masa kan asarar rayuka da dama da aka yi a Jihar, a kwanakin baya.

Gwamnan ya kara da cewa, duk da kokarin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, na karfafa tsarin tsaron kasar, ya kamata Sarakunan Gargajiya su yi amfani da nasu hanyoyin da za su kawo karshen rashin tsaro.

“Ina kira ga Sarakunan Gargajiya, da su hada kan al’ummar kasar nan, domin kare al’umma, shugaban kasa, ya himmatu wajen samar da ayyuka, kuma mu a kananan hukumomi; mun dukufa wajen aiwatar da dukkanin manufofinsa, kana kuma; nuna shugabanci na gari shi ne abin da muka sanya gaba,” in ji shi.

Dangane da dalilin ziyarar Gwamna Bago, ya ce; sun je jihar ne, domin jajanta wa gwamnati da jama’a, dangane da haduran jiragen ruwa da na tankar mai da rashin tsaro da suka yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama tare da raba mutane da dama da gidajensu.

Ya ce, “Mun zo ne, domin mu yi wa dan’uwanmu ta’aziyya tare da karfafa masa gwiwa, mu kuma bayar da gudunmawar kudi da addu’o’i, da kuma bai wa iyalan wadanda iftila’in ya afka hakuri tare yi musu ta’aziyyar rashin da suka yi”.

“Gwamna Bago, na daya daga cikin mafi kyawun cikinmu, mafi haske, mai kuzari kuma wanda ya san makamar aiki” in ji shi.

Gwamnan Jihar Neja, Bago da Etsu Nupe da Shugaban Masu Rike da Sarautun Gargajiya na Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, duk sun yaba da ziyarar da gwamnonin masu ci suka kawo musu jihar.

Bago ya yi tir da kalubalen tsaro da dimbin bala’o’i da suka addabi jihar, ya kuma ce; gwamnati ta dukufa wajen ganin an samu zaman lafiya.

Gwamnonin da suka ziyarci Minna, sun hada da na Jihohin Delta, Kogi, Ebonyi, Imo da kuma Legas, yayin da Mataimakan Gwamnonin Jihohin Jigawa, Kebbi da Sokoto, suka wakilci nasu gwamnonin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

November 14, 2025
Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya
Manyan Labarai

Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

November 14, 2025
Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
Manyan Labarai

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

November 13, 2025
Next Post
Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

November 14, 2025
Abin Da Ya Sa NPA Ta Yi Hadaka Da ‘Snake Island Port’ -Dakta Dantsoho

Abin Da Ya Sa NPA Ta Yi Hadaka Da ‘Snake Island Port’ -Dakta Dantsoho

November 14, 2025
Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

November 14, 2025
Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

November 14, 2025
Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

November 14, 2025
Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

November 13, 2025
Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

November 13, 2025
Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

November 13, 2025
Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya

Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya

November 13, 2025
Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

November 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.