Wasu daga cikin mayan Masana’antu Masu Zaman Kansu da ke Arewacin kasar nan, sun yi maraba da matakin da Gwamnatin Tarayya ta yanke na sanya harajin kaso 15 a cikin dari, na shigo da Man Fetur daga ketare.
Sun bayyana cewa, wannan matakin na Gwamnatin Tarayya, abu ne da ya dace, musamman bisa nufin kara samar da Man a cikin kasar da kara karfafa fannin samar da Man da kuma Iskar Gas a cikin kasar, wanda hakan zai kuma, kara bayar da damar yin gasa a tsakanin Masana’antun da ke a cikin kasar.
- Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
- NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna
Muhammad Nura Madugu, wanda shi ne shugaban kungiyar MAN reshen ta Sharada-Challawa da ke a jihar Kano ya bayyana haka a yayin ziyarar da kungiyar ta kai ga mahukuntan rukunin Matatar Mai ta Dangote da ke in Abuja.
Ya bayyana cewa, masu masana’antun za su gaba da goyawa tsare-tsaren da Matatar Man ta Dangote ta samar, musamman domin kara samar da ci gaba mai dorewa da daga darajar Man da ake samar wa a kasar, wanda hakan zai sanya a kai Nijeriya zuwa wani mataki na duniya.
Kazalika, Madugu ya kara da cewa, ‘ya’yan kungiyar sun aminta da tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya ta samar domin kara ciyar da fannin gaba tare da kuma cin gajiyar da ke a fannin.
A cewarsa, damar kauwancin da ake samu daga fannin an same ta ne, saboda yadda Matatar ta Dangote, ke sarrafa danyen Mai wanda kuma ‘ya’yan kungiyar, ke son ganin sun amafana da hakan daga Matatar ta Dangote.
Madugu ya ci gaba da cewa, wasu daga cikin bangarorin da kungiyar za ta amfana daga Matatar ya ce, sun hada da, Man da ake sarrafawa daga danye Mai, Man Dizil, Kalanzir, Man Jirgin Sama da kuma Iskar Gas, samfarin LPG.
Sauran ya ce, sun ne, sanadaran naphtha, bitumen, ethylene, propylene da sauransu.
Kazalika, ya kuma jinjinawa Shugaban rukunin Matatar Man ta Dangote, Aliko Dangote, bisa namijin kokarin da ya yi, na kafa Matatar Man a kasar nan.
Tawagar ta kungiyar MAN, ta kuma karrama Dangote da mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman a bangaren hudda da jama’a da kuma jagorar aikin rukunin Matatar Madam Fatima Wali-Abdurrahman da babbar lambar yabo.
A kwanan baya ne, Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya amince da sanya kaso 15 a cikin dari kan Man Fetur da Man Dizil da ake shigowa da su cikin kasar daga ketare, inda danganta tsarin, a matsayin matakin sarrafa Mai a cikin kasar da kuma rage yin dogaro kan makamashin da ake shigowa da shi, daga waje.














