Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma babban jigon jam’iyyar hadaka ta ADC, Malam Nasir El-Rufai, ya ce jam’iyyar ta tsara ka’idoji ga shugabanninta da ‘yan takararta kafin zaben 2027.
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da ‘yan jarida a ranar Asabar a Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara.
- Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
- Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu
Ya ce jam’iyyar ADC na da niyyar kawo canji mai dorewa a Nijeriya. Ya zargi gwamnatin APC karkashin shugabancin Bola Tinubu da yaudara da cin hanci da rashawa da kuma rashin gaskiya.
A cewarsa, kundin tsarin mulkin ADC ya fi dukkan wani kundin tsarin jam’iyyun siyasa a Nijeriya, saboda ya hada da dabi’un shugabanci.
“Shugabancin jam’iyyar a halin yanzu yana aiki kan dokar dabi’a da kowanne shugaba da jami’in da aka zaba dole su rattaba hannu. Wannan zai tabbatar da cewa wadanda suke karkashin ADC suna mai da hankali kan kyakkyawan shugabanci, babu karkatar da kudaden jama’a, babu cin hanci, kuma babu cin zarafi,” in ji shi.
El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa.
Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan jam’iyyar, yana cewa, “APC ba za ta bar ku ku tafi cikin sauki ba, ku yi hankali.”
Haka kuma, ADC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara, wanda mataimakin sakataren gudanarwa na kasa na jam’iyya ya shirya, don karfafa hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyya da kuma karfafa musu gwiwar yin rajista da samun katin zabe.












