Cristiano Ronaldo, kyaftin ɗin tawagar Portugal, na fuskantar yiwuwar dakatarwa har ta wasanni biyu a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, bayan an kori fitaccen ɗan ƙwallon daga wasan da suka sha kashi 2-0 a hannun Jamhuriyar Ireland ranar Alhamis. Wannan rashin nasarar ya zo ne a lokacin da Portugal ke neman tabbatar da tikitin shiga gasar, lamarin da rashin bugawar Ronaldo zai iya shafar su.
Rahoton ESPN ya nuna cewa Ronaldo ya fara karɓar katin gargaɗi ne a minti na 61 saboda mahangurba da gwuiwar hannu da ya yi wa O’Shea na Ireland. Amma bayan duba VAR, alƙalin wasa ya soke katin gargaɗin ya ba shi jan kati kai tsaye. Wannan shi ne jan kati na farko da Ronaldo ya samu a wasa 226 da ya bugawa Portugal, duk da cewa an kore shi sau 13 a matakin kulob.
- Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati
- Ronaldo Zai Daura Aurensa Na Farko A Rayuwa Tare Da Budurwarsa Georgina
A dokokin ladabtarwar FIFA, jan kati kai tsaye saboda mahangurɓa ko duka yana iya haifar da dakatarwa har wasanni uku. Saboda haka, Ronaldo ba zai taka leda a wasan gaba ba, sannan ana iya ƙara masa hukunci idan kwamitin ladabtarwa ya ga laifin ya tsananta. Har ila yau, hukuncin dole ne ya kasance a wasannin gasa, ba a wasannin sada zumunta ba.
Portugal ta shiga wasan ne da ƙwarin gwuiwar cewa nasara za ta samu nasara da gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka, da Kanada da Mexico. Sai dai ƙwallaye biyu na Troy Parrott suka tarwatsa burinsu a Dublin.
Duk da haka, Portugal har yanzu tana saman rukunin F da maki biyu a gaban Hungary, kuma za ta iya kammala tikitin shiga gasar idan ta doke Armenia a ranar Lahadi.














