Shugaban ƙungiyar Fulani makiyaya ta ƙasa (MACBAN), Baba Othman Ngelzarma, ya bayyana cewa Musulmin da suka rasa rayukansu a Zamfara, da Katsina da Sokoto sun ninka adadin Kiristocin da aka kashe a tsakiyar Nijeriya (Middle Belt). Ya yi wannan bayani ne a tattaunawarsa da gidan talabijin ɗin Channels, yana mai ƙalubalantar iƙirarin da ke nuna cewa ana kai wa Kiristoci hari ne musamman a rikice-rikicen da ke faruwa a sassa daban-daban na ƙasar.
Ya ce matsalar tsaro ta rikiɗe zuwa rikici mai cike da rikitarwa da ya ƙunshi bambancin ƙabila, da addini, da rikicin manoma da makiyaya, wanda ya ƙara haifar da ta’addanci, da garkuwa da mutane da kashe-kashe.
- Kungiyar Fulani Ta MACBAN Ta Nesanta Kanta Daga Zanga-zangar Matasa
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina
Ngelzarma ya ce rikice-rikicen ba yanayi ɗaya suke da shi , domin suna bambanta daga wuri zuwa wuri. Ya tunasar da harin 2017 a Sardauna, Taraba, yankin da Kiristoci suka fi yawa, inda sama da makiyaya 700 aka kashe cikin kwanaki biyu, yana mai tambaya kan dalilin da ya sa ba a duba irin wannan adadi da biyu. A Benue kuwa, ya ce tashin hankali ya karu tun daga shekarar 2014 lokacin aiwatar da dokar hana kiwo a fili, wanda ya kara tayar da kura tsakanin manoma da makiyaya a jihar da Kiristoci ke da rinjaye.
A jihar Filato, Ngelzarma ya ce rikicin ya fi kama da matsalar ’yan asali da masu shigowa, amma ba rikicin addini kai tsaye ba. Ya zargi gwamnatin jihar ta yanzu da ƙara ruruta wutar rikici a Mangu, yana mai cewa lamarin bai kai haka ba a gwamnatocin baya. Ya bayyana cewa makiyaya sun daɗe suna fuskantar hare-hare a yankin, wanda ya saɓa da labarin da ake yaɗawa cewa sune ke kai hari.
Game da Boko Haram, ya ce kashi 90 cikin 100 na waɗanda suka mutu Musulmai ne, duk da cewa jama’a da dama suna ganin Kiristoci ne ake kai wa farmaki. Ya ce hankalin duniya ya fi karkata kan sace-sacen Chibok ne saboda yankin Kiristoci ne, alhali mafi yawan ɗaliban Dapchi da aka sace Musulmai ne. Ya yi nuni da cewa hakan ya nuna rikicin ya fi rikitarwa fiye da yadda ake yaɗawa.
Ngelzarma ya kuma ce mutanen da suka mutu a Zamfara, da Katsina da Sokoto sun ninka na tsakiya Nijeriya, kuma mafi yawansu Musulmi ne. Ya buƙaci a kalli matsalar tsaron Nijeriya da idon basira da fahimtar bangarori da dama, yana mai cewa idan za a yi hukunci kan rikicin, ya kamata a kira shi da kisa bil’adama gaba ɗaya, ba kisan addini guda ɗaya ba.













