A baya-bayan nan, firaministar Japan Sanae Takaichi, ta furta wasu kalamai na tayar da husuma, dangane da yankin Taiwan, yayin da take tsokaci a majalisar dokokin kasarta, inda ta ambata yiwuwar aiwatar da matakan soji a zirin Taiwan. Wannan ne karo na farko da shugabar Japan din ta yi yunkurin tsoma baki cikin batun Taiwan, tun bayan da Japan din ta ci tura a yakin duniya na biyu, shekaru 80 da suka gabata, yunkurin da ya yi muni matuka.
A jerin kwanakin baya-bayan nan, kasar Sin ta sha tuntubar kasar Japan tare da nuna kin amincewa da matakin na Japan na tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta, da haifar da illa ga odar duniya, da tushen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Japan.
A jiya Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya kira, tare da ganawa da jakadan Japan dake kasar Sin, inda ya jaddada cewa, kasar Sin za ta mayar da martani kan duk wani mataki na kawo cikas ga neman dinke dukkanin sassan kasar Sin.
A shekaru 80 da suka gabata, jama’ar kasar Sin sun cimma nasarar yaki da maharan kasar Japan, da kawo karshen mamayewar yankin Taiwan da kasar Japan ta yi. A halin yanzu kuma, gwamnatin kasar Sin da jama’arta, ba za su amince da duk wani mataki na illata moriyar kasar Sin, da kawo cikas ga neman dinke dukkanin sassan kasar Sin ba.
An yi kashedi ga manyan shugabanni, da jami’an gwamnatin kasar Japan, da su yi biyayya ga ka’idoji bisa tarihi, da batun yankin Taiwan daidai da takardun siyasa hudu wadanda Sin da Japan suka daddale, da janye yunkurin tsoma baki cikin batun Taiwan, da kuma daukar matakai don kawar da illar da wannan batu ya haifar. Kasar Sin za ta mayar da martani da ya dace, idan har kasar Japan ta dauki mataki marar dacewa. (Zainab Zhang)














