Assalamu alaikum. Malam, idan mutum ya yi wasa da matarsa a watan Azimi har Maziyyi ya fito, yaya matsayin wannan Azimi nasa?
Aziminsa yana nan, sai dai a ce ya kaucewa sake yin hakan a nan gaba domin akwai Malaman ma da suke ganin idan mutum ya fitar da Maziyyi Aziminsa ya karye, akwai kuma wasu Malamai su ma da dama da suke ganin Azimin nasa bai karye ba. Don haka wajibi ne mutum ya yi kokarin fita daga wannan sabani na Malamai, amma dai Aziminka yana nan. Ala ayyu halin, tunda ba ka da karfin zuciyar mallakar kanka da har za ka fitar da Maziyyi, to sai a ce ka daina wasa da iyalinka, don kuwa kana da raunin da wata rana za ka iya saduwa da iyalin naka.
Assalam Malam. Don Allah kamar yadda muke tunawa da matattu, su ma suna tunawa da mu?
Kwarai kuwa! Matattu suna tunawa da mutum ta hanyoyi guda biyu, kodai idan su masu rai din sun yi wani abin kirki a gare su ko kuma su yi wani abu na farin ciki, kamar yi musu addu’a ko sadaka ko kuma wani abun alheri, to za su iya ganin wannan abun alherin. Haka kuma, idan ba a yi musu addu’a ko sadaka a nan ma sukan bukaci hakan a gare su musamman ga ‘ya’ya ko ‘yan’uwansu da ke nan duniya, shi ne yasa da zarar sun ga wani abun alheri sai su tambaya, Allah Ya ce da su; sadaka ko addu’a aka yi muku, wani lokaci kuma su da kansu sukan bukaci hakan shi yasa ma wasu daga cikin ‘yan’uwansu kan yi mafarki da su suna yi musu ishara cewa suna bukatar wani abu daga gare su kamar yadda Ibn Kayyum ya bayyana a cikin littafinsa, Hadil Arwa ko kuma Arruh.
Haka zalika, kamar da da uba ko da uwa ko kuma ‘yan’uwa na iya ziyarar juna bayan sun mutu ta hanyar ruhi, musamman ma idan sun hadu wajen aikata wani abin alheri. Za su iya ziyartar juna ta hanyar wannan ya je kabarin wannan shi ma wancan ya je kabarin wannan amma fa a ruhi kamar yadda na fada a baya. Sannan wani lokaci mutum yakan rika yin mafarki da iyayensa ko ‘ya’yansa akai-akai yana jin shaukin haduwa da su, wannan alama ce da take nuna cewa sun kusa su hadu.
Assalamu alaikum. Malam, mutum ne yake yin Azimi amma ba ya yin Sallah, mene ne matsayin Azimin nasa?
Babu shakka Aziminsa yana nan zunubinsa na rashin yin Sallah kuma shi ma yana nan, kowanne yana nan a matsayinsa. Kamar mutumin da yake yin ajiya ne a asusun banki ko kuma a ce yana yin ajiya a bankuna daban-daban, idan ya kwashe na wannan asusun, na wancan asusun na nan babu abinda zai same shi. Saboda haka dai ladan Aziminsa yana nan, zinibinsa kuma na rashin yin Sallah shi ma yana nan, ma’ana zunubinsa na rashin Sallah yana nan, ladan Aziminsa shi ma yana nan. Kawai dai duk wanda ya samu kansa a irin wannan hali, ko shakka babu abin tausayi ne sai dai a yi masa addu’a Allah Ya shirye shi.
Salam. Malam, don Allah wai da gaske ne idan mutum ya karya Azimi guda daya sai ya rama sittin?
Sosai kuwa, idan har mutum ya karya Azimi da gangan sai ya rama daya ya kuma yi sittin, idan ba da gangan ba ne ko kuma mantawa ya yi ya ci abinci ko ya sha ruwa, wasu Malaman na ganin Aziminsu ya karye wasu kuma na ganin Aziminsa yana nan. Amma a takaice dai duk wanda ya karya Azimi yana sane ko da gangan, ko shakka babu sai ya rama dayan da ya karya ya kuma yi na kaffara dai-dai har guda sittin a jere babu hutawa ko tsayawa.
Assalamu alaikum. Malam, tafiya ce ta kama ni daga Kano zuwa Abuja, ajiye Azimi a wajena Sunnah ce ko Mustahbi?
Ganin dama ne, don kuwa Allah cewa ya yi “ku yi Azimi shi ya fi” wasu Hadisai kuma cewa suka yi “ka ci abinci shi ya fi”. Saboda idan mutum zai yi tafiya ya tabbatar ba zai sha wuya ko haduwa da wani abu da zai tayar masa da hankali ba, to sai ya yi Azimi, amma idan ya tabbatar da cewa idan ya yi tafiya zai sha wahala, ya bar Azimin shi ne mafi alheri a wajensa, amma dai matafiyi shi ne ya sani; daga Kano zuwa Zariya daga Kano zuwa Kaduna ko Abuja duk mutum zai iya shan Aziminsa, ya rage gare shi idan yana ganin yin Azimin ya fi masa sauki ko kuma ya ci abinci shi ne mai zabi domin kuwa lafiyarsa da kwanciyar hankalinsa su ake nema.
Hukuncin Yin ‘Charting’ Ga Matan Aure
Assalamu alaikum. Malam muna so a bayyana mana hukuncin shiga facebook ga matar aure.
Wa alaikumus salam. Zance mafi shahara shi ne, duk abin da zai amfane ta za ta iya yi a facebook, saboda asali a Shari’ar Musulunci, duk abin da mutane suke aikatawa a mu’amalarsu ta yau da kullum halal ne, mutukar ba a samu wani nassi wanda ya haramta ba, ko kuma ya kasance cuta tsantsa. Haka ma idan mafi rinjayansa barna ne, ka ga Facebook kuwa babu wani nassi da ya haramta shi, sannan ba cuta ba ne tsantsa, tun da ana iya samun ilimin addini ta wannan kafa. Sai dai, dole ta guji yin ‘charting’ da wadanda ba muharramanta ba, in ba malamin da ta yadda da iliminsa da tsantseninsa ba, za ta yi masa fatawa, saboda akwai maza da yawa da suke bi ta hanyar ‘charting’ don lalata matan auren da ba su da kamewa. Wannan ya sa barin ‘charting’ da mazan da ba muharramai ba, ko kuma wadanda suke neman auran matar, zai iya zama wajibi, saboda hakan yana kaiwa zuwa ga barna, duk abin da yake kaiwa zuwa ga barna, zai iya zama haramun ko makaruhi, kamar yadda malaman Musulunci suka tabbatar. Allah ne mafi sani.
Amsawa daga:
Dr. Jameel Zarewa
Iddar Macen Da Ta Yi Bari
ambaya
Assalamu alaikum malam mutumne yasaki matarshi bayan sati biyu sai tai bari to malam ya iddanta zai kasance nagode
Amsa
Wa alaikumus salam.
Idan cikin da ta yi barin sa, ya zama halitta kamar kai ko hannu ko kafa toh ta gama idda da wannan barin wannan shi ne rajihin zance, kamar yadda ya zo cikin (kash shaful kinaa’i 5/413).
Sai dai mazhab na Malikiyya sun saba ma wannan kaulin da cewa in dai an yi barin tarerren jini ko da babu wata halitta da ta bayyana a cikin sa to idda ta kare, kamar yadda yazo cikin littafin ( muktasarul khaleel 1/130)
Nafi gamsuwa da ra’ayin malikiyya don fadar Allah cikin suratul dalaak aya ta hudu.
Wallahu A’alam
Amsawa daga:
Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed
Nafilolin Rawatib A Takaice
Tambaya
Salaamun alaikum, Malam Dan Allaah ina son ingancin wadannan sallolin nafilan:
1- Raka’ah 12 a wuni, da aka ce Allaah zai gina wa mutum gida a Aljannah.
2- 2- Raka’a takwas kafin sallar azahar da bayan sa wuta ba zai ci shi ba.
3- Raka’ah hudu kafin sallar la’asar
Amsa
Wa alaikum assalam, tabbas hadisi ya tabbata cewa: “Duk wanda ya yi sallolin nafila raka’ioi 12 Allah zai gina masa gida a cikin Aljanna”.
Zaid bin Arkam daya daga cikin Sahabban Annabi (SAW) ya fassara wadanann nafiloli da sifa kamar haka:
Raka’a biyu kafin sallar asuba, raka’a hudu kafin sallar Azahar, raka’a biyu bayanta, raka’a biyu bayan sallar Magriba, sai kuma raka’a biyu bayan sallar Isha.
Ragowar abin da ka fada ban san shi ba a hadisai, rashin sanina kuma baya nuna babu shi.
Allah ne mafi sani
Amsawa daga:
Dr. Jamilu Zarewa