A Bai Wa Matan Nijeriya Kashi 38 Cikin Dari Na Duk Mukamai – Amina Mohammed

Matan

Daga Zubairu M. Lawal,

Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, ta yi kira ga masu fada a ji da ke rabon mukaman siyasa a Gwamnatin Nijeriya da su rika kebe rabon mata a duk mukaman gwamnati da za a raba ga mata.

Ta ba da shawarar cewa a rika kebe wa mata kashi 38 cikin 100 domin su amfana da da kuma bayar da gudunmawa wajen harkokin cigaban siyasan a Nijeriya.

Hajiya Amina Muhammad ta ce mata suna taka mahimmiyar rawa a siyasar Nijeriya musamman lokacin zabe da yakin neman zabe. Amma da zarar an kafa Gwamnati to maza suke amfana da dukkan mukamana gwamnati da kashi 90% a Nijeriya.

Ta kara da cewa kamata ya yi a samar da gurabe da za su zamana mukaman na mata ne din-din-din.

Hajiya Amina Muhammad ta ce a bangaren zababbun kujerun mulki mata sukan samu tsaiko. Saboda ba a cika samun matan da suke samun nasara a zabe ba.

“Ya kamata a ce mata suna samun nasara mai inganci ga kujerun da ake zaben, daga matakan kananan hukumomi zuwa jihohi har a dangana da zuwa tarayya.” In ji ta.

Exit mobile version