Abba Ibrahim Wada" />

A Barcelona Zan Yi Ritaya, Cewar Messi

BARCELONA, SPAIN - AUGUST 04: Lionel Messi of FC Barcelona waves to the crowd prior to the Joan Gamper trophy friendly match at Nou Camp on August 04, 2019 in Barcelona, Spain. (Photo by David Ramos/Getty Images)

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi ya ce ya so ya bar Barcelona a shekarar 2013, amma yanzu ya yanke hukuncin cewar a kungiyar zai yi ritaya daga buga wasa saboda babu kungiyar da zai koma a halin yanzu.

Kyaftin din na tawagar kasar Argentina, ya fada a wata hira da wani gidan radiyo a birnin Barcelona mai suna RAC 1 ya yi da shi, inda ya ce ba a kyauta min ba da aka tuhume ni da laifin kin biyan haraji.

Mahukuntan Spaniya ne suka tuhumi Messi da mahaifinsa da laifin cewar sun yi kokarin kin biyan haraji kuma Messi ya ce Barcelona ba su yi masa laifi ba, amma a lokacin ji ya yi gwara ya bar Spaniya da buga wasa.

Ya kuma kara da cewar a lokacin kungiyoyi da dama sun yi zawarci na, amma an kasa cimma yarjejeniya ne saboda kowa ya san cewar bana son barin Barcelona kuma inason cigaba da kafa tarihi a kungiyar.

Messi ya koma Barcelona makarantar rainon ‘yan kwallo La Masia tun yana da shekara 13, ya kuma fara buga wa babbar kungiyar wasa yana da shekara 16 daga nan ne kawo yanzu ya zama dan wasan da ya fi ci wa Barcelona kwallo a raga, yana da 604 kuma shi ne na biyu a yawan buga wa kungiyar wasanni bayan Dabi.

Messi ya kara da cewar babu wata sabuwar yarjejeniya da ya yi a Barcelona, bayan wadda za ta kare a shekara ta 2021, amma a Barcelona zai kammala wasannin kwallon kafa kuma kyaftin din na Barcelona ya ce yana kaunar kungiyar, kuma iyalansa suna jin dadin zama a Spaniya, saboda haka zai ci gaba da zamansa.

Exit mobile version