Abubakar Abba" />

A Cikin Shekaru 12 Na Yi Musayar Jarirai Sama Da 500 –Tsowar Ma’aikaciyar Jinya

Wata tsohuwar ma’aikaciyar jinya mai suna Elizabeth Mwewa dake a kasar Zambiya ta nemi gafara akan zunuban data tabka har na tsawon shekaru sha biyu tana aiki a wani Asibitin kwararru dake kasar.
Elizabeth ta nemi gafarar ce a lokacin tana kwance akan gadon dake jinyar cutar daji.
Laifin da ta aikata a cikin tsawon shekaru sha biyun shine tana musaya jariran da iyayen su mata suka haifa a Asibitin, inda ta ce ta yi musayar jarirai sama da 5000 don kawai nishadi.
Ta ce, tana fama da matsananciyar cutar kansa wadda tasan mutuwa kawai take jira a yanzu shi ya sanya ta tona kanta domin neman yafiyar iyayen data yi musayar jariran su a lokacin da suka haifhu a Asibitin.
Elizabeth ta ce, bana son in mutu in shiga wuta shi yasa naga ya kamata in tuna kaina don neman yafiyar wadanda na musanya masu jariran su.
Ta ce sanadiyar hakan ta janyo mutuwar aure da dama bayan da ma’uratan suka je yin gwajin kwayoyin halittar su kuma, inda aka gano jinin matan iyaye ya sha banban dana jariran da suka Haifa.
Elizabeth ta kara da cewa, ta kuma janyo iyaye mata da dama sun shayar yayan da basu suka haife ba.
Elizabeth ta shawarci iyaye mata da suka haihu a Asibin daga shekarar 1983 zuwa shekarar 1995 su gaggauta zuwa yin gwajin kwayoyin hallitar su, don gudun kada suci gaba da kula da yayan da ba nasu ba.

Exit mobile version