Connect with us

LABARAI

A Da Malam Hausa Sun Banzantar Da Marubuta Hausa Ne-Farfesa Abdalla

Published

on

A makon jiya mun tsaya inda FARFESA ABDALLA ya ke shaida wa Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, yadda a ka yi ya samu damar gabatar da makala a wata jami’a da ke kasar Jamus, lamarin da ya fara bude ma sa hanyar da ta kai shi ga zama farfesa a karo na biyu. Ga yadda su ka dora a zantawar:

A ka ba ni tikiti na tafi Jamani na je na gabatar da ita (makalar). To, kafin na taho sai da ita matar ta ce ka taho mi ni da litattafan soyayya na Hausar nan. Na je na jido su da yawa, na yi kwali guda na je na kai. Bayan na gama gabatar da takardar na ce ga litattafai da ki ka ce na taho mi ki da su na kawo. Sai ta ce, ‘nawa ne?’ Sai na ce ‘me ki ke nufi nawa ne? Ai ni kyauta na kawo mi ki.’ Sai ta ce, a’a, ai su na da ‘budget’ na sayen litattafan, sun rasa wanda zai je ya zakulo mu su litattafan ne. tunda ya ke yanzu na zo da su, za su kirga su, sai su biya ni kudin, kuma haka a ka yi. Ni ban yi tsammanin za su biya ni ba, amma dai a ka biya ni da wasu kudade wadanda dai masu dan nauyi ne har na je na sayi wasu takalma da na ke sha’awa na saya, wadanda na san ba zan iya saya da kudina ba. To, ka ga yadda a ka yi kenan.

To, a haka a hankali-a hankali sai Kenya, sai abu ya rika; sai Ingila. Haka dai sai gayyata ta rika zuwa; ‘zo ka gabatar da wannan’, amma ba a tada gayyata a Najeriya na zo na gabatar da wata mukala a wata jami’a kan wannan abin ba, sai kalilan kawai… amma na je taruka kasashe-kasashe na ‘international conferences’ guda 35; na je Morocco, na je Itofiya, na je Senegal duk a kan adabi. Ni ban damu a kira ni ko a nan Najeriya ko kar a kira ni ba, amma dai duniya ta san akwai wannan abu…

 

To, a ganinka me ya sa su a Najeriya ba su damu kira ba?

Saboda a arewacin Najeriya an banzantar da abin, a na ganin rubuce-rubucen nan da finafinan duk shashanci ne. A Kudu da ma ba su san me mu ke yi ba. Ba su da sha’awa. Idan za su yi bincikensu a kan adabin Afrika sai dai ka ji abiinda a ke cewa ‘post colonial African literature’, kamar su Wole Soyinka, Chinua Achebe. Shikenan a kan irin wadannan su ke yi. Nan Arewa kuma idan ba irin su Abubakar Gimba ba da irin wannan, ba a ganin mutum ya na wani rubutu ba; ba wani wanda zai zauna ya yi nazari a kan Bala Anas Babinlata ko Sa’adatu Baba Ahmad ya ce ai su na yin wani rubutu ba; ni ne kadai na dauke su da daraja na ke cewa abinda su ke yi gaskiya ya na da muhimmanci.

To, kuma su zakakuran binciken, wato manya-manyan malaman namu masu nazarin wadannan abubuwa, a lokacin sun banzantar da su sun ce shashanci a ke yi. Sai da Braham Fanes ma ya fara tattara wadannan litattafan ya yi ‘library’ katuwa, sannan jami’ar Bayero su ka fara tunanin su ma bari su dan debi kadan haka su ajiye. ’Yan kadan ma su ka ce; ai bari a dan debi ’yan kadan dai a ajiye, hana-rantsuwa! Amma da na je gidan Graham a Ingila, wani zuwa da na yi, ya kai ni gidansa ya nuna min wani daki, gabadayan garu guda duka litattafan Hausa, don ya bada kudi duk wata shida duk litattafin da ya fito (ya na nan Danladi ya na tara ma sa litattafan. Danladin ya na Zoo Road kusa da Gidan Buhari). Duk littafin da ya fito, a tattara a kai ma sa (shi Graham), amma mu ba ma haka. Mu na BUK, mu na kilomita 10 daga shi Danladin, amma Danladi idan ya tattara duk wata shida zai tattara litattafan ya aika wa Farfesa  Graham, wanda an tattara su an saka su a Jami’ar London. Kuma idan ka je ‘Library of Congress America’ su na nan. Yanzu idan ka shiga Library of Congress ka ce Bala Anas Babinlata, Ado Ahmad Gidan Dabino, Balaraba Ramat Yakub, duk za ka ga litattafansu a Library of Congress a USA, an dauke su da muhimmanci. Akwai wani mutum a na kiran shi Dabid Hogan, shi kuma yawo ya ke yi, duk shekara zai rika yawo kwararo-kwararo a Kano, lungu-lungu, su Jakara Bookshop ne ya na zuwa ya na tattaro litattafai ya na kai su London ya na sayar da su da tsada!

To, ka ga duniya ta san abinda a ke yi, amma mu a nan gurin ba a san abinda mu ke yi ba. To, amma da ma haka lamarin ya gada. To, amma mu ba mu damu ba; abokanmu na duniya su ne su ke tallafa ma na. ban taba biyan kudi na je taro a kasar waje ba. Duk taron da na je, kira na a ke yi a biya ni. Ba sa biyan wani kudin Laraba, saboda su ba su gaji wannan ba; wai ka ji an ce ga naka, babu wannan! Amma za a ba ka otel, za ka ci abinci, za a ba ka kudin dan zirga-zirga, shikenan da na tikiti. To, kuma wannan ba ma shi ne ya fi muhimmanci ba; muhimmancin shi ne a kira ka… Kuma za ka ga an kashe makudan kudi a kanka, amma sai ka ji an ce da kai minti 20 fa a ka ba ka (a wajen gabatar da makalarka). Minti 20! Duk abinda za ka fada, ka fada a minti 20. Ka na kai wa minti 15 za a rika azalzalar ka, ka yi sauri ka gama, saboda akwai wadansu. To, idan an gama sai a tace-a tace, sannan sai a buga littafi. To, shi malamin jami’a babu abinda ya ke sha’awa irin a buga ma sa littafi.

To, wata rana a shekara ta ko 2011 ne? Sai mu ka je Jamani a tafiyar da mu ka ni da Ado Gidan Dabino Jami’ar Hamberg na gabatar da makalolina a kan dai irin rubutun da na ke yi tun daga 1999, wanda ya hada da adabi na rubutu da adabi na fim, daga bayan-baya kuma da adabi na waka. To, duk rubutun da na yi, a kan wadannan na yi; samuwarsu, yanayinsu, sigoginsu, juyawarsu, dangantakarsu da wani adabin kuma na duniya da kuma yadda mutane su dauke su da yadda matasa su ka dauke su. Duk a kan wannan ne tun daga wajen 1999 har za ka iya cewa zuwa wajen 2010. Wato shekara 11 abinda a ka yi ta yi kenan. To, a 2011 mun je Jamani na gabatar da makala a kan dai abinda na saba. To, bayan na gabatar da makalar, akwai wata mace a cikin taron a na kiran ta Nina Fablak, mutuniyar Polish ce, da a ka gama sai ta tambaye ni ta ce da ni, na taba zuwa Polland? Na ce, ‘a’a, na taba zuwa ba’. Ta ce, ‘ka na son ka zo Polland?’ Na ce, ‘me zai hana?’ Ta ce, ‘abinda ka gabatar ya na da muhimmanci kuma zan so a ce mutanen jami’ata a Polland sun san da wannan. Saboda haka za mu gayyace ka ka zo ka koyar na tsawon zango guda, wato wata uku a Polland.’ Na ce, ‘ai na san ki a jami’ar Bayero’. Ta kan zo Bayero. To, akwai wata kungiya da su ke yi ta manazarta Hausa na Turawa, sai su ka hada da Bayero a ciki. Akwai Italiya, akwai Jamani, akwai Polland, to sai a ka hada da Bayero. Na ke jin duk shekara biyu ko uku ne sai a je kasar wata jami’a a daya daga cikin kasashen su gabatar da abubuwansu, to sun zo Kano wata rana shekara biyu kafin lokacin da na hadu da ita a Jamanin. Da a ka ce za a zo a yi wannan taro, sai mu ka yi murna mu ka ce ‘ai wannan dama ce ta mu zo mu gabatar da makalun da su ka dame mu’. Mu na zuwa sai a ka da mu ba za ta yiwu ba; wai ai sai dan ahalin abin shi ne zai gabatar da takarda a wurin. Sai ’yan sashen ma, wato ba a yarda wani wanda ya fito daga wani sashen wanda ba na Hausa ba ya zo ya gabatar ba. Za ka iya zuwa taro idan ka na so, amma ba a yarda ka gabatar da mukala ba!

 

A makon gobe idan Allah Ya kai mu za mu ji yadda a ka karke da wannan takaddama kan gabatar da mukala a wajen wannan taro a jami’ar ta Bayero tsakanin bangaren Farfesa Abdalla da bangaren ahalin

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: