Abba Ibrahim Wada" />

A Daina Hada Ni Da Ronaldo —Salah

Dan wasan gaba na Liberpool Muhammad Salah, ya bayyana cewa bai kamata mutane su dinga tunanin hadashi da dan wasa Robaldo ba saboda kowanne acikinsu yadda yake buga kwallonsa daban.

Salah, mai kwallaye 9 a gasar zakarun turai ya bayyana cewa wasan karshe da zasu fafata a tsakanin Real Madrid da Liberpool ba tsakanin Ronaldo da Salah bane tsakanin kungiyoyin ne.

Yaci gaba da cewa dashi da yan wasan kungiyar ta Liberpool ne sukayi aiki tukuru sukaga sunzo wannan mataki kamar yadda shima Ronaldo da ragowar yan wasan Real Madrid sukayi aiki da gaske wajen ganin kungiyar tazo wasan karshe.

Ya ce yana buga wasa a babbar kungiya a duniya mai cike da tarihi da nasarori kamar yadda shima Ronaldo yake bugawa babbar kungiya a duniya mai cike da tarihi da burin lashe manyan kofuna.

Yaci gaba da cewa babu dan wasan da zai iya kai wata kungiya wasan karshe shi kadai dole sai da hadin kan ragowar yan wasa da magoya baya da kuma mai koyarwa da shugabanni da kuma likitoci.

Salah yace yana fatan lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallo na duniya na wannan shekarar inda yace yasan duka larabawan da suke duniya suna goyon bayansa domin ganin ya lashe wannan kyautar.

A ranar 26 ga wannan watan ne dai za’a fafata wasa tsakanin kungiyoyin biyu a filin wasa na Olympic dake birnin Kieb dake kasar Ukraine.

 

Exit mobile version