A Daina Jingina Wa Ubangiji Laifi Kan Tabarbarewar Tsaro A Nijeriya –Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su dauki laifin lalacewar zaman lafiya a kasar nan. Su kuma daina dorawa Allah laifi.
Olusegun Obasanjo, ya bayyana hakan ne a jawabin Kirsimati da ya yi a bukin Kirsimati na wannan shekarar wanda ya gudana a Cocin, Christ the Glorious King (CCKG), da ke babban dakin karatu na, ‘Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL), Oke-Mosan, da ke Abeokuta, ta Jihar Ogun.
Tsohon Shugaban kasan, ya bayyana fatan da yake da shi ga ‘yan kasar nan a 2019, yana mai cewa, “Tabbas shekarar za ta zama shekara ce mai albarka a kasar nan.”
Obasanjo, ya bayyana jin dadin sa a kan yanda addu’o’in suka gudana, ya ce sam halin da kasar nan take ciki a halin yanzun ba abin karfafa gwiwa ne ba.
“Lamarin yana kara tabarbarewa ne a kullum. Na je Kaduna, inda na yi zaton a can lamarin ba kamar na nan ne ba. Amma sai mutane a can din suka shaida mani cewa, akwai matsalar ta tsaro, ana sace mutane, da kashe-kashe duk suna ta aukuwa. In har mun rasa zaman lafiya, to ba Allah ne Ya kawo mana shi ba, mune muka haddasa shi. Shi ya sanya na ji dadi da irin wa’azin da Bishop ya gabatar, da kuma wa’azin da ya yi a kan zaman lafiya. Tabbas wannan shi ne lokacin da ya dace da irin wannan wa’azin na zaman lafiya, wannan lokaci ne na samar da zaman lafiya.”

Exit mobile version