A Duba Ambaliyar Da ‘Yan Karkara Ke Yi Zuwa Birane

A kullum ta Allah akasarin manyan birane a Nijeriya kara bunkasa suke yi ta hanyar samar da manyan sabbin gine-gine da kuma kayata su, amma kuma yankuna Karkara na kara lalacewa da zagwanyewa.

Akwai kiyasain da ya nuna cewa, kusan kaso 70 na mutum Miliyan 200 da ake da su a  kasar nan, mutanen Karkara ne, amma har zuwa yanzu an yi watsi da su, babu wani cigaba a tattare da su a wannan kasa da muke ciki. Wannan dalili ne ya karfafa musu rika yin hijira zuwa birane, musamman ma Matasansu domin samun walwala da ayyukan yi.

Kazalika, wadannan dalilai ne suka hana Matasan Karkarar tsayawa su dage wajen yin wadataccen noma, wanda zai amfane su ya amfani kasa baki-daya, suke tururuwar zuwa Birane domin yin aikace-aikacen da za su samu kudi, musamman a gidajen matan aure da dattijai.

Ko shakka babu, sanin kowa ne cewa, rayuwar mazauna Karkara a kullu yaumin kara tabarbarewa take yi, musamman a lokutan wannan gwamnati.

Duk dai da cewa, kowace gwamnati na da irin nata tsare-tsaren da kuma ayyukan da take tsara yi, domin inganta rayuwar al’ummar Karkara, amma aiwatar da ayyukan ko tsare-tsaren su ne babban jan aiki a wajenta.

Wadannan dalilai ne suka sanya ake yawan yin watsi da ayyukan da ake bijiro wa da su a yankunan wannan Karkara, ake kuma cigaba da mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan a sauran Birane.

Haka nan, Jihohi da sauran Hukumomin Gwamnati, wadanda ke da ruwa da tsaki wajen aiwatar da ire-iren wadannan ayyuka ke yin burus da su, babu abinda ya shafe su, kamar ma a matsin babu wani abu da ke faruwa.

Sun manta, ba ya ga nauyin da ke kansu na tabbatar da cewa, wadannan ayyuka na Karkara na tafiya da sauri ka’in da na’in, wajibi ne kuma su sake kirkiro wasu sabbin ayyukan don sake dakile batun yawan yin hijira daga Karkarar zuwa Birane tare da rage yawaitar talaucin da ke addabarsu, amma sam abin bah aka yake ba.

Kirkirar Kananan Hukumomi 774 da aka yi a fadin kasar nan, an yi su ne da kyakkyawan manufa, domin kawo cigaba a kowane lungu da sako na Tarayyar Nijeriya.

Kowace shekara ana ware biliyoyin Nairori a kasafin kudi na tarayya, jihohi da kuma Kananan Hukumomi, amma har yanzu mutane na zaune cikin wani mummunan hali na rashin ababen more rayuwa, musamman ma mutanen Karkara. Saboda haka, babu wani abin kirki ko a zo a gani da za a iya nunawa cikin wadannan makudan kudade da ake warewa a duk shekara.

Kazalika, ko da ayyukan Mazabu wanda Majalisar wakilai ta bijiro da su domin taimakawa yankunan Karkara, babu wani sauyi da suka kawo na a zo a gani. Shi yasa kwana-kwanan nan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ikrarin cewa, Naira tiriliyan daya da Gwamnatin Tarayya a kashe a wadannan ayyuka na Mazabu, bai ga wani abin arziki ba.

Haka nan, wani rahoto na kwanan nan, ya ja hankalin ‘yan Nijeriya cewa, kudaden da aka batar wajen samar da wutar lantarki a Karkara, sama da Naira Milyan 80.6, har yanzu wadannan Kauyuka na nan cikin duhu, babu wuta.

Sa’annan, an kashe biliyoyin Nairori wajen gina Cibiyoyin kula da harkokin lafiya guda 30,000 a fadin kasar nan, amma ko daya bisa uku daga cikinsu yanzu ba sa aiki. Kazalika, har izuwa yanzu babu guda cikin masu kula da wadannan Cibiyoyi da suka karyata wannan rahoto kan wannan zargi da ake yi musu.

Bugu da kari, Shugabannin Siyasa kadai suna tunawa da mazauna Karkara ne a lokutan kakar zabe ta taso tare da yi musu ire-iren wadannan alkawarurruka na samar masu da ayyukan kayan more rayuwa, amma da zarar sun shiga Ofis sai su manta da su.

Yanzu haka, lalacewar ta kai zai yi wuya ka samu hanyar da mota za ta iya bi ko Asibiti ko kuma wasu abubuwa na more rayuwa a Karkara. Wannan ne yasa al’ummarsu a koda-yaushe, ke barin gurarensu zuwa Birane domin samun saukin rayuwa.

Domin kawo karshen wadannan matsaloli a Karkara, wannan Gidan Jarida ke yin kira da a duba ambaliyar da ‘yan karkara ke yi zuwa birane ta yadda za a sake sabunta wannan tsari na yunkurin ciyar da Karkara gaba, a tsarin harkokin gwamnati.

Da farko dai, wajibi ne gwamnoni su baiwa Kananan Hukumomi cikakken ikon da tsarin mulkin kasa ya ba su. Musamman a wannan lokaci da gwamnoni ke rike makoshin kudaden wadannan Kananan Hukumomi, da ta kai ga cewa Shugaban Karamar Hukuma, ba shi da ikon kashe sama da Naira 50,000, ba tare da gwamna ya sahale masa. Sannan, dole ne gwamnoni su daina kakaba wa mutane Shugaban Karamar Hukumar da ya ga dama ba, ya kamata a kyale mutane su rika zabar wanda suke so ya jagorance su.

Kazalika, ya zama wajibi Gwamnatin Tarayya ta rika aiwatar da bincike akan Hukumomin da ke da alhakin kula da cigaban wadannan yankuna na Karkara.

Wajibi ne a kawo karshen zaluncin da Shugabannin Siyasa ke yi wa al’ummar da ke zaune a Karkara, ta hanyar karbe ayyukan Mazabu daga hannu ‘Yan Majalisa, wanda suke yin amfani da su suna azurta kawunansu.

Sannan, tunda dai an gano cewa, sama da kaso 70 na al’ummar wannan kasa na zaune a yankunan Karkara, ya zama wajibi a kirkiri Ma’aikatar Cigaban Karkara a Gwamnatin Tarayya da kuma jihohi, domin maye gurbin ayyukan da ya kamata Kananan Hukumomi su yi.

Exit mobile version