A Dubi Lamarina – Wanda Ya Yi Wa APC Tattaki Yana Fama Da Ciwon Kafa

Daga El-Mansur Abubakar,Gombe

Wani magidanci mai suna Dahiru Buba, dan asalin karamar hukumar Dukku a Jihar Gombe, wanda ya yi tattaki zuwa Abuja daga garin su na Dukku, saboda Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, ya na fama da ciwon kafar da ya ke nema jamiyyar ta ta dubi lamarinsa.
Dahiru Buba ya yi tattaki ne, inda ya isa Abuja cikin kwanaki 15, ya kuma samu tarba daga shugabannin jam’iyyar lokacin Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya na Sakataren Jam’iyyar na kasa, kuma an ba shi satifiket na nuna kwazo da son jam’iyyar.
Magidancin ya ce, yanzu haka ya na fama da ciwon kafar da ya ke son a taimaka ma sa, domin tun bayan da ya yi wannan tattaki har zuwa yanzu bai samun komai ba, banda kudin mota da a ka ba shi na dawo wa gida da wannan satifiket da uwar jamiyyar ta ba shi.
Ya ce, ya na neman tallafi tun da jam’iyyar APC ce ta ke mulki, kuma ita ya yi wa tattakin, saboda kishi. Don haka ya na son su yi ma sa hanya ya samu lafiya, kuma ya mallaki gida a garinsu, sannan ya samu hanyar dogaro da kansa, domin a halin yanzu karatun ’ya’yansa ma ba ya iya biya, saboda rashin kudi, baya ga matsala irin na rayuwa.
Dahiru, maigidanci ne da ya ke da matan aure biyu da ’ya’ya bakwai, kuma a cewarsa, kamar yadda kowa ya ke sa ran ya mori siyasa idan a ka kafa gwamnati, hakan ta sa ya yi wannan tattaki, don shi ma ya shaida cewa jam’iyyar APC mai adalci ta ci zabe kuma shi ma a taimaka ma sa.
A cewarsa, idan a ka taimake shi, zai ji dadi, sannan kuma a duba halin da ya ke ciki, wanda kafarsa ba ta da lafiya, ta na bukatar kulawa, don kar ta zama an kasa shawo kan ciwon.
Sannan ya ce, a Jihar Gombe ma ya na bukatar Gwamna Inuwa Yahaya ya shiga tsakani, don ya taimake shi, saboda shi ma wakilin Shugaban kasa ne kuma Wakilin APC.
Daga nan sai ya roki duk wani masu fada-a-ji a jam’iyyar ta APC da idan sun ji kukansa, su yi ma sa hanya ya samu taimakon da ya kamata, don ceto kafafunsa daga jinyar da ya ke fama da ita.

Exit mobile version