Connect with us

MANYAN LABARAI

A Fara Duban Watan Muharram Gobe Lahadi –Sarkin Musulmi

Published

on

Fadar Sarkin Sokoto ta bada sanarwar da a fara duban watan Muharram din sabowar shekarar Hijarar Annabi Muhammad (S) ta 1440 daga gobe Lahadi 9 ga watan Satumba.

A cikin takardar da Farfesa Sambo Junaidu ya sanya wa hannu, na cewa gobe Lahadi wanda ya yi daidai da 29 ga watan Zul Hajji za a fara duban watan sabowar shekarar Hijara ta 1440.

‘Saboda haka muna fatan dukkan al’ummar Musulmi za su sanya ido wajen duban watan, duk kuwa wanda ya samu nasarar ganin jinjirin watan sai ya sanar wa Dagacin garinsu, shi kuma sai ya sanarwa fadar Sarkin Musulmi.’ inji Farfesa Sambo




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: