Connect with us

MANYAN LABARAI

A Fassara Yarjejeniyyar Zaman Lafiya Zuwa Harsunan Nijeriya –Kungiya  

Published

on

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Legacy Initiative International ta bukaci a fassara yarjejeniyyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin manyan addinai biyu na Musulmi da Kirista, zuwa yarukkan Nijeriya saboda duk al’ummar kasar nan su samu damar karanta yarjejeniyar.

 

Mista Kenny Martins shine jagoran kungiyar, ya yi wannan kiran yau Juma’a a garin Legas, a cewar shi fassara wannan yarjejeniyyar zai matukar taimakawa al’ummar kasar nan wajen samar da zaman lafiya, musamman a yayin da muke fuskantar zabukkan shekara 2019.

 

A ranar Talatar da ta gabata ne Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na uku wanda shine shugaban Jama’atul Nasril Islam, da kuma shugaban Kungiyar Kiristoci ta kasa Rabaran Samson Ayokunle, sun hada hannu waje guda, don cimma yarjejeniyyar zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai biyu.

 

Mista Martins yana cewa, Yakamata kungiyar Jama’atu da CAN, su fassara wannan yarjejeniyyar saboda sauran al’ummar da basa fahimtar harshen turanci su ma, su samu damar karanta wannan yarjejeniyyar mai matukar muhimmanci, musamman da yake muna fuskantar zabukkan shekarar 2019.
Advertisement

labarai