Abba Ibrahim Wada" />

A Hankali Zamu Koma Mataki Na Daya – Klopp

klopp

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp, ya bayyana cewa yana da yakinin a hankali kungiyarsa zata koma mataki na daya kamar yadda take a baya idan har suka ci gaba da samun nasara a wasanninsu.
Bayan buga wasanni biyar a jere ba tare da samun nasara ba, kungiyar Liberpool ta huce haushinta a kan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a ranar Alhamis din data gabata in da ta lallasa ta da ci 3-1.
Nasarar da Liverpool ta samu ta hannun ‘yan wasanta Roberto Firmino, Sadio Mane da kuma Aledander Anorld, ta bata damar komawa cikin rukunin kungiyoyi hudu na farko a gasar Premier da maki 37, maki 4 tsakaninta da Manchester City dake kan gaba a halin yanzu.
Yanzu haka dai Manchester United ce ta biyu da maki 40 a gasar ta Premier bayan rashin nasarar da tayi har gida da 2-1 a hannun Sheffeild United a ranar Laraba, Leicester City ce kuma ke biye da Mnachester United din a matsayi na uku da maki 39.
Klopp ya ce idan har ‘yan wasansa suka ci gaba das aka kwazo a wasanninsu na gaba tabbas zasu kai inda suke so kuma ya bayyana cewa watakila kungiyar ta shiga kasuwa domin sayan dan wasan baya wanda zai taimakawa kungiyar.

Exit mobile version