Muazu Hardawa" />

A Inganta Masana’antu Da Kudin Da Ake Biyan ’Yan Siyasa –Garba Noma

Inganta masana’antu  a Nijeriya na daya daga cikin kudirorin da wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ta yi alkawari tun lokacin da ta ke yakin neman zabe, amma duk da kasancewar ta samu nasarar kafa gwamnati a karkashin jam’iyyar APC an wayi gari a kullum masana’antun suna kara durkushewa matasa kuma suna rasa ayyukan yi. A saboda haka MUAZU HARDAWA ya tattauna da ALHAJI GARBA MOHAMMED NOMA JARMAN BAUCHI, shugaban kamfanin dab’i na RAMADAN PRESS da ke Bauchi inda suka tattauna game da dalilan da suka haifar da rashin ci gaban masana’antu a Nijeriya alhali gwamnati na ikirarin fitar da kudi don taimakawa masana’antu su tsaya da kafar su, ga yadda hirar ta kasance:

 

Yallabai me za ka bayyana mana kan halin da masana’antu ke ciki a Nijeriya game da dorewar su?

Sunana  Alhaji Garba Mohammed Noma dan kasuwa kuma dan siyasa wanda ya ci moriyar gwamanti ta fannin inganta kafa masana’antu, abin da zan ce shi ne idan da ace an ci gaba da tsari kamar yadda aka yi mana a shekaru 40 da suka wuce wajen tallafawa game da gina kamfanoni  da an ci gaba da wannan tsari da yanzu muna da masana’antu masu yawa a kowane waje. Mun koyo wannan aiki a India kuma gwamnati ta tallafa mana da kudin da bai taka kara ya karya ba a wancan lokaci a kan wanda muke da shi har muka kafa wannan kamfani na Ramadan Press wanda yanzu ke da cikakkun ma’aikata masu aiki a wannan kamfani kusan 165 da kuma ma’aikatan wucin gadi  kusan 30 jimla muna da ma’aikata kusan 200.

Idan da an ci gaba da bin tsari irin wanda ya gabata a shekarun baya da yanzu muna da kamfanoni irin su Ramadan a Bauchi kusan guda 20 ko fin haka,  kuma ko da duk basu rayuba a samu guda goma amma siyasa ta shigo ta lalata lamurra wajen ganin an dauki dukiya dare daya an wadata mutane ba tare da sun yi komai bat a hanyar basu manyan mukamai ana biyan su makudan kudi daga karshe kuma idan aikin ya kare a bar su cikin damuwa su gaza komawa karamin matsayi don neman abinci.

 

Akwai bashin kafa masana’antu da gwamnati ke cewa tana bayarwa  don tallafawa kun taba samu?

Kwarai mun taba samu amma bamu ci gaba da nema ba kuma yawanci wadanda ake yi domin su basa samu kuma muma bamu ci gaba da nema ba.  Ya kamata ace kowace gwamnatin jiha ta kafa hukuma da wakilinta ba kwamishina kawai ba musamman mai lura da yadda kanana da manyan masana’antu ke cin moriyar irin wannan bashi ba tare da ruwa mai nauyi ba,  daga Abuja  a sa ido a tabbatar da cewa sun karbi irin wannan bashi cikin sauki, don dama gwamnatin jiha ta san ka ba gwamnatin tarayya ba kuma ita gwamnatin jiha ita ne za ta tsaya ta tabbatar irin wannan taimako an ci moriyar sa ba tare da an sha wahala ba. Amma sau da yawa irin wannan dama ta taimakawa masana’antu tana zuwa daga gwamnatin tarayya amma mutanen mu basa samun cin moriyar irin wannan.

Amma da a ce gwamnati ta shiga cikin lamarin da kowa zai amfana don dukkan harkar da gwamnati ta shiga an fi samun nasara madadin a ce kamfani ko mutum shi ne kurum ya shiga ya fara neman irin wannan tallafin.

 

Baka ganin ka’idojin da ake gindayawa ne ke tsanani akan irin wannan bashi?

Akwai wannan amma idan da ace gwamnati ta shigo da kowa zai fi cin moriyar lamarin, musamman a yanzu siyasa ta lalata lamarin  ganin yadda da ace an bi ka’ida an kafa irin wadannan kamfanoni goma sha biyar da yanzu bakwai suna raye. Misali kudin da aka kashe a kan nada PA da SA a gwamnatin baya da wancan kudin an kashe su wajen gina masana’antu manya da kanana da yanzu an samu ci gaba sosai. Saboda a yanzu abin da ke faruwa sai a dauki yaro wanda bai san komai ba sai hayaniyar siyasa ko karamin ma’aikaci dan matakin albashi na biyar a bashi mukamin siyasa wanda za a rika biyansa albashi sama da dubu dari ko a bashi mukami na matakin albashi na 17 ba ya aikin komai ana bashi makudan kudi, ranar da tafiyar ta kare kuma a sauke shi ya kasa komawa sana’ar da ya faro ko ya gada sai ya kama gararamba shin wannan ya dace ace mutum ba abin da ya sani ana bashi makudan kudi? Madadin haka da tallafa masa aka yi ya fadada sana’ar da ya ke yi kuma yana hidimar siyasa sai a wayi gari ya kara yin karfi yadda zai tsaya da kafafun sa. Amma a yanzu mutane sun saba da samun kudin banza sun kashe zuciyar su ba za yi wani abu da zai tallafi rayuwar su a gaba ba idan tafiyar siyasa ta kare an sauka da milyoyin naira an wayi gari matsalolin yau da kullum sun cinye kudin sai a koma gidan jiya a ci gaba da talaucewa sai a shiga hanyoyi marasa kyau na ganin lallai sai an koma yadda aka fito mukaman da aka tsaya sun sake dawowa.

 

Me ake nufi da samun kudin banza?

Idan da an kashe kudin da gwamnatin da ta wuce a kan PA da SA da an kashe su kan masanaantu 50 da yanzu a kalla 20 suna aiki, da wancan kudin da an sa a masana’antu kowace masarauta da sai ta samu a kalla masana’antu 10, don haka duk wanda ke samun karami aka bashi kato hakika gobe ba zai koma matsayinsa ba an sakaltashi daga inda ya saba ciyar da iyalansa idan abu ya gagara ba zai dawo baya ba. Don duk wanda ya dandana ni’ima idan ka dawo da shi baya sai ayi tsiya da shi ka ga an lalata shi kenan an sakalta shi yana samun kudin banza bai yi aikin komai ba wannan ko addini bai yarda da haka ba.

 

Wane sirri ke gareku wannan Kamfani na Ramadan ke gudana amma da dama sun rushe a Bauchi?

Wannan yardar Allah ce ba za mu ci fariya ba muna bin shari’a ne mu nema a bamu mu aika ta mu yi fada wa kan mu, idan an bamu aiki mu sa ido mu yi kuma da kan mu muke sayo kaya mu sarrafa duk wannan yardar Allah ce, saboda mu kasuwanci mu ke yi bama kwangila sai aiki mu yi a biyamu, Ramadan ta ginu da naira dubu 60 ta fara yanzu tana da naira milyan shida zuwa milyan 60 ko fiye da haka. Idan da bamu bi lamarin a hankali tare da bin doka ba da bamu kawo haka ba, mun yarda mu yi aiki a biya mu hakkin mu da haka muka ginu har muka kawo inda muke a halin yanzu.  Amma kamar yanzu abin da ke faruwa mutum na samun dubu sha biyar idan siyasa ta gangaro kan sa sai ka ga an kaishi matsayin da ya ke samun dubu 300 ya samu kudi kawai a matsayin siyasa idan ba ya yi fada wa kan sa ba duk abin da ya samu yana cin kaji da man shanu  da hawa manyan motoci duk lokacin da suka yanke sai yadda hali yayi.

 

Me ka ke gani faduwar darajar naira da yawan karbar kudin haraji da gwamnati ke yi haifar a Nijeriya?

Hakika ya jawo matsala sosai saboda kaya sun yi tsada mutane basu da kudin saye bayan haka ga matsalar da ake samu game da yadda kamfanonin ke fiskantar matsala na sayo kayan da za su sarrafa. Don haka dole kayan su yi tsada gwargwadon tsadar kayan da aka sayo da kudin waje, kuma haka za a sayar wa mutanen kasa, su kuma mutane ba su da kudi don haka kasuwar ke zama ba dadi ba ciniki ga kaya ba masu saye, shi yasa a kullum lamurra ke komawa baya ‘yan kasuwar ke karyewa saboda rashin tsari game da yadda za su gyara lamurra su tsaya kan kafafun su.

Kamar yanzu mun biya harajin mu gaba daya mun gama sai aka fito da wasu sabbin hanyoyi dag hukumar tattara haraji kasa aka sake ce mana sai mun sake biyan naira milyan uku kafin a bamu takardar shaida, gaskiya yawan kawo kudi da gwamnati ke yi yana haifar da rusa masana’antu yadda a kullum ake kuka da halin da ake ciki na karbar kudi ba kan gado don haka ake samun lalacewar lamurran kamfanoni da sauran su. Ya kamata gwamanti ta dauki mataki kan matsalar da ake ciki game da masana’antu don a samu gyara matsalolin da ake fiskanta na rushewar masana’antun wanda ke haifar da rashin aikin yi a tsakanin mutane,  a tashi a tsaye a tallafi masana’antun don su tsaya da kafar su matasa su samu abin yi su daina yin barazana ga tsaron kasa, kuma duk tallafin da suke bukata a tabbatar an samar musu kuma ya kai hannun su kai tsaye don su yi aikin da ya dace kasa ta amfana.

Exit mobile version