Daga Rabiu Ali Indabawa,
Rahoton ya ce galibi lauyoyi ne ke da alhakin bayar da cin hanci don yanke hukunci mai kyau aksarinsu a cikin al’amuran zabe da na siyasa ne. Rahoton mai taken, ‘Inded of Corruption Inded: Report of a pilot surbey’, ya auna ayyukan cin hanci da rashawa ne a fannoni hudu, da suka hada da bangaren zartarwa, majalisa, bangaren shari’a, da kuma kamfanonin kasuwanci masu zaman kansu.
Hanyar ta kasance ana tafiyar da ita ta hanyar gogewa ne maimakon tambayoyin da suka shafi fahimta game da rashawa, kamar yadda aka auna daga sikeli daga 0 zuwa 100, tare da 0 da ke wakiltar lamarin da ba cin hanci da rashawa ba, sannan guda 100 na nuna” Cikakken Cin Hanci Da Rashawa ” Kididdigar ta kuma nuna tarin bayanai a kan ayyukan cin hanci da rashawa dangane da tayin kudi da wanda ba na kudi ba daga ma’aikatan da suke aiki a Ma’aikatun Gwamnatin da manajojin Daraktoci na kungiyoyi (MDA’s) wadanda su ma suna shiga cikin wannan binciken.
Bangaren Shari’a
Binciken ya kara da cewa, ragowar wadanda aka amsa 114 ko kuma kaso 12.65 cikin 100 daga 901 da aka amsa a bangaren shari’a, ba su nuna matsayin su ba. “Kudin da ke cikin almundahana a cikin wannan sashe an kasafta su cikin kudin da aka nema, aka bayar ko aka biya. Jami’an kotu ciki har da alkalai ne ke neman hakan, yayin da bayar da cin hancin da kuma biyan kudi daga lauyoyi da masu shigar da kara, ”in ji rahoton.
“Jimillar kudin da masu gabatar da kara na bangaren shari’ar suka bayar da rahoton kamar yadda cin hanci da rashawa suka nema, aka bayar kuma aka biya tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020 ya kai Naira biliyan 9,457, 650,000.00 (N9.457).” Binciken ya kara da cewa kimanin mutane 78 daga cikin masu shari’a 901 da aka kawo karar sun ba da rahoton fuskantar tayin ko bayar da cin hanci ga tsarin shari’a. Daga cikin wannan adadin, wadanda ake kara 63 lauyoyi ne da aka bincika don sun biya ko sun bayar da Naira biliyan 5.77 a matsayin cin hanci don yanke hukunci.
Daga cikin lauyoyi 63 da ake kara, lauyoyi mata sun biya ko kuma suka bayar da Naira miliyan 918 a matsayin cin hanci, yayin da takwarorinsu maza suka biya ko suka bayar da Naira biliyan 4.815 a matsayin cin hanci don yin tasiri a kan wani hukunci. “Wadannan kudaden sun kai kashi 9.71 bisa 100 da kuma kashi 50.92 bisa 100 na jimillar kudin da masu rahoton bangaren shari’a suka ruwaito. Lauyoyin sun bayar da rahoton kashi 60.63 na cin hanci da rashawa da masu gabatar da kara na bangaren shari’a suka bayar kuma suka biya, ”in ji rahoton.
Goma sha daya daga cikin alkalai 123 da aka bincika, sun ba da rahoton fuskantar tayin ko biyan Naira biliyan 3.307 da Naira miliyan 392.3 a matsayin cin hanci.
Bangaren Dokoki
Rahoton na ICPC ya binciki masu bayar da bayanai (MDA) 399 wanda kashi 26 ko 6.51 cikin 100 suka bayar da rahoton MDA dinsu ta da ta biya rashawa jimillar Naira miliyan 86 don ziyarar kula da majalisa. A cewar rahoton, kimanin kashi 52 cikin 100 na wadanda aka amsa daga MDA din sun ce sun samar da masaukin otal ne domin sa ido a kan harkokin majalisa, kuma kashi 48 cikin 100 sun amince da gudanar da ziyarar majalisar ta hanyar sufuri.
Haka nan, kashi 35 da kashi 27 cikin 100 na masu gabatar da kara na MDA sun ce sun taimakawa ziyarar sanya ido kan doka ta hanyar daukar ma’aikata, nishadi, kyauta da kuma biyan kudi bi da bi.
Bangaren Zartarwa
ICPC ta ce yayin da ka’idar gudanar da aikin ga jami’an gwamnati ta hana neman ko karbar wata kadara ko wata fa’ida a kan duk wani abu da wani jami’in gwamnati ya aikata, kimanin kashi 38 daga cikin kashi 399 da suka amsa MDA a kashi 9.5 cikin 100 sun samu jimillar Naira miliyan 3 a matsayin kyauta don aikin da ya shafi kwangila. Rahoton ya lura da cewa kashi 45 na 399 MDA da aka amsa sun bayar da rahoton cewa a cikin kwarewar su, ma’aikata sun sami ma’aikata bisa ga dangantakar siyasa.