Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa wani bayani a shafinsa na sada zumunta a jiya Asabar, inda ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Najeriya, bisa zargin wai “gwamnatin Najeriya ta bar ‘yan ta’adda suna yi wa masu bin addinin kirista kisan kiyashi.”
Labarin ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta na Najeriya. A Facebook, masu amfani da yanar gizo na Najeriya sun nuna bacin ransu, tare da isar da “gaisuwa” ga shugaba Trump, wadda ba zan maimaita a nan ba, ganin yadda aka yi amfani da kalmomi masu kaushi. Sai dai daga cikinsu, na ga wani mai amfani da yanar gizo da ya yi tambaya kamar haka: “Su wane ne Amurkawa za su kaiwa hari?”
Hakika ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda da na ‘yan bindiga a Najeriya, sun shafi dimbin mutane, da bangarori, wadanda suke bin mabambantan ra’ayoyi, kuma suke zaune a wurare daban daban. Wannan yanayi ya haifar da gagarumin kalubale ga kokarin da sojojin Najeriya suke yi na yaki da ta’addanci cikin shekarun da suka gabata. Saboda haka, ko da yake, yayin da shugaba Trump ke barazana, ya yi amfani da kalmomi masu kaushi kamarsu “yin luguden wuta,” “nuna cikakken karfi wajen kai farmaki,” da “kai wani harin da zai zama mai faranta rai”, amma idan da gaske sojojin Amurka za su kutsa kai cikin harabar Najeriya don yaki da ta’addanci, lallai cikin sauri za su fuskanci matsala.
Duk da cewa suna da karfi a fannin aikin soja, amma harinsu zai zama tamkar amfani da igwa ne wajen kashe sauro. Duk wani fifikon da suke da shi ba zai dore ba. Saboda haka, a zahiri wannan tambayar da wani mai amfani da yanar gizo ya yi, ta nuna rashin hankali cikin kalaman shugaban Amurka.
Sai dai kalaman sun dace da halayya, da salon musamman na shugaba Donald Trump. Wani lokaci, da gangan ya kan yi amfani da kalmomi, da aikace-aikace marasa ma’ana wajen samar da yanayi na rashin tabbas, ta yadda zai samu damar matsawa wani lamba, don tilasta masa ya yi wani aiki. Wannan dabara ce da wasu masanan kasar Amurka ke kira da “ka’idar mahaukaci”, watakila ta dace da halayyar shugaba Trump, abun da ya sa yake ta amfani da ita wajen kula da harkokin waje.
Kana wannan batu na yin barazanar kai hari ya dace da halayyar kasar Amurka. Kasa ce wadda ba ta mai da hankali a kan neman gano gaskiya ba, balle ma la’akari da bayanan da Nijeriya ta gabatar dangane da zargin da aka yi mata. Kai tsaye an yi fatali da ikon mulkin kai na Najeriya, da dokokin kasa da kasa, da ra’ayoyin kasashen yankin da ake ciki. A ganin kasar Amurka, tana iya tsoma baki a duk wani aiki, da aikata yadda ta ga dama, kuma idan za ta iya yin amfani da karfin tuwo wajen tilasta wani, to ba za ta taba tattaunawa da shi ba. Kawai kasar tana kokarin aiwatar da mulkin danniya ne a duniya.
Amma, a cewar wasu masana, “ka’idar mahaukaci” ba ko yaushe take yin tasiri ba. Saboda idan wani ya dade yana kwaikwayon mahaukaci, to, ba za a ci gaba da tsoronsa ba. Kana mulkin danniya na kasar Amurka shi ma ba zai dore ba, idan aka yi la’akari da yadda kasashe masu tasowa ke tasowa cikin sauri a zamanin da muke ciki.
Ko ta yaya ya kamata Amurka ta daidaita kalamanta da ayyukanta? Kuma ta wace hanya ya kamata kasashe daban daban su yi mu’ammala da juna?
Na farko, ya kamata mu tabbatar da daidaito tsakanin mabambanta kasashe, da kuma bin dokokin kasa da kasa. Na biyu, ya kamata mu daukaka ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, da neman daidaita harkoki ta hanyar yin shawarwari, maimakon tayar da rikici. Na uku, ya kamata mu dora muhimmanci kan jin dadin jama’a, ta yadda ba za a tsaya ga kula da mutanen gida kadai ba, wato a hada da al’ummun sauran kasashe. Ya kamata a lura da hakkinsu da bukatunsu. Wadannan abubuwa suna cikin shawarar da kasar Sin ta gabatar, dangane da inganta jagorancin duniya.
Watakila kasar Amurka ba ta yarda da wadannan ka’idoji ba tukuna, amma tabbas wata rana za ta amince da su. (Bello Wang)














