Bilkisu Xin ta CRI Hausa" />

A Kara Yin Gargadi Ga Adam Silver Na NBA: Kada A Hada Batun Mulkin Kan Kasa Da Na ’Yancin Bayyana Ra’ayi

Bayan babban manajan kungiyar wasan kwallon kwando ta Rockets ta birnin Houston ta kasar Amurka Daryl Morey ya ki neman gafara kan kalamai marasa tushe da ya yi game da yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, kuma hukumar kwallon kwando ta Amurka (NBA) ta bayyana cewa, ba za ta yanke hukunci kan Morey ba, kwamishinan NBA Adam Silver ya nuna goyon bayansa a fili kan ikon ’yancin bayyana ra’ayi da Morey ke da shi. Game da haka, jiya Talata tashar dake watsa wasannin motsa jiki ta CCTV ta babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ta kara bayar da sanarwa cewa, za ta dakatar da watsa dukkan gasannin kwallon kwando na NBA.
Adam Silver da ma makamantansa sun yi kalaman kuskure bisa dogaro da ’yancin bayyana ra’ayi, amma dukkan kalaman dake kalubalantar mulkin kan kasa da zaman karkon al’umma ba su da alaka da batun ’yancin bayyana ra’ayi. Bayanan da Adam Silver da Daryl Morey suka yi sun bayyana cewa, suna da boyayyiyar manufa, kuma sun kasance masu girman kai kuma marasa ladabi.
A cikin sabuwar sanarwar da Adam Silver ya bayar, ya ce zaman daidai wadaida, da nuna girmamawa da kuma ’yancin bayyana ra’ayi su ne ra’ayin NBA. Amma, kamata ya yi a nuna daidaito da girmama juna. Kalamai marasa tushe da Daryl Morey ya yi ba su girmama mulkin kai da mutuncin al’ummar kasar Sin ba, ra’ayin da Adam Silver ya nuna ma bai nuna daidaito ba, a maimakon haka, ya yi kalaman dake kalubalantar mulkin kan kasar Sin, da bakanta ran jama’ar kasar Sin.

Exit mobile version