Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano ce ake zaton zata Fara Shugaban Karamar Hukumar na farko a tarihin Jihar Kano Mai Matsayin Farfesa wanda ake sa ran zaba a zaben Kananan Hukumomi da za’a gudanar nan da kwanaki biyar masu zuwa.
Farfesa Yusif Mohammed Sabo gogaggen likita ya Zama Wanda ke yiwa Jam’iyyar APC takarar shugabancin Karamar Hukuma a kakar zaben da ake fatan gudanarwa ranar 16 ga watan Janairun Shekara ta 2021.
Al’ummar Karamar Hukumar Bichi sun bayyana gamsuwarsa tare da Alfaharin cewa cikin kananan Hukumomin Jihar Kano 44 sune zasu Fara zabar Farfesa a Matsayin shugaban Karamar Hukuma.
Farfesa Yusif Mohammed Dabo na wannan jawabi ne alokacin zagayen yakin neman zaben da yake, inda wannan rana ta Litinin ya ziyarci babbar mazabar nan ta Barume, inda ya gana da Shugabannin Jam’iyyar APC, kokas, Malamai ya kuma gaisa da iyayen Kasa, inda suka tabbatar masa da ci gaba da yi Masa fatan alhairi. Kamar yadda Aliyu Musa Sabo ya shaidawa LEADERSHIP A Yau.