CRI Hausa" />

A Karon Farko Kwararrun WHO Sun Jinjinawa Sin Game Da Tallafinta Ga Binciken Da Suka Gudanar

A makon jiya ne kwararrun da hukumar lafiya ta duniya WHO ta tura birnin Wuhan, domin gudanar da bincike game da asalin cutar COVID-19, suka kammala aikin su a birnin. Mambobin tawagar dai sun jinjinawa yadda Sin ta gabatar da komai a bayyane, wanda hakan ya sanya tawagar ta masanan, yin watsi da jita jitar da aka rika yadawa, domin bata sunan kasar Sin.

A ranar Lahadi 14 ga watan nan, jaridar “The New York Times” ta Amurka, ta wallafa cikakkiyar zantawa da Dr. Peter Daszak, mamba a tawagar kwararrun ta WHO, wanda yayin tattaunawa da shi, ya ce da isar su birnin Wuhan, gwamnatin Sin ta samar musu da dukkanin dama, ta gudanar da aikin da ya kai su cikin nasara.
Ya ce sun samu bayanai, da alkaluma, irin wadanda ba za a iya samun su a wajen kasar ba. Ya buga misali da yadda aka ba su damar ganawa da ‘yan kasuwar kayan ruwa dake birnin na Wuhan, da bayanai game da daga inda suke sayo kayayyakin da suke sayarwa, da ma alakar kasuwar da wadanda suka fara harbuwa da annobar COVID-19.
Dr. Daszak ya jinjinawa gudummawar jami’an Sin, wadda ta kai su ga cimma cikakkiyar nasara. Yana mai cewa, bayan rufe kasuwar ta kayan ruwa a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2019, da kuma ran 1 ga watan Janairun shekarar 2020, hukumar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkin su ta kasar Sin, ta aike da masana kimiyyar ta, domin binciko duk wasu alamu da za su haskaka tushen cutar. Har ila yau, jim kadan da bullar cutar, masana kimiyya na kasar Sin, sun yi gaggawar kammala daukar samfura sama da 900 daga kasuwar, don taimakawa sauran ayyukan bincike na gaba.
Dr. Daszak, ya kuma yi fatan cewa, dukkanin ayyukan binciken da za a gudanar a nan gaba, za a yi su ne karkashin ilimin kimiyya, maimakon siyasantar da al’amura. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version