Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) a ranar Talata ta ba wa kamfanonin sadarwa na kasar nan makonni biyu don toshe layukan wayar salula (SIM) wadanda ba su da rajista da Lambobin Shaida na dan Kasa (NIN) Wanda hukumar tattara bayanan ‘yan kasa ke badawa wacce akafi sani da (NIMC).
Sanarwar ta yi gargadin cewa duk wani kamfanin sadarwa da ya ki bin umarnin da aka ba shi, ya sani lasisin aikinsa na tangadi ko kuma zai sha azabar tara mai yawa.
A makon da ya gabata ne Gwamnatin Tarayya, ta hanyar Hukumar sadarwa ta NCC, ta ba da umarnin dakatar da yin sabbin rajistar layin wayar salula SIM don ba da damar tantance layin SIM din da ke da rijista .
Amma masu ruwa da tsaki a masana’antar sadarwa sun bayyana fargabar cewa kimanin mutane masu amfani da layin miliyan 25 ne wannan umarnin zai shafa.