A Kira Masu Laifi Da Laifinsu, Ba Da Kabilarsu Ba – Hon. Ahmad

Maganar tsaro, magana ce mai mahimmanci, wacce ta kamata ta damu kowa, domin zaman lafiyar al’umma shi ne tushen komai.

Abin bakin ciki ne yanda lamarin tsaron ya ke kara jagwalgwalewa, ya ke kara damewa da har a halin yanzun ya kai matsayin da ya ke bayar da tsoro. Kamar yanda nake gayawa wadanda mukan tattauna da su a kan maganar tsaro, magana ce da ta shafi Duniya bakidaya. Al’amari ne da ya ke ta kara tabarbarewa a duk in da ka kalla. Amma abin da ya shafe ka kai tsaye shi ne ya kamata ya fi damunka.
Hon. Aminu Ahmad kenan mai wakiltar mazabar Makarfi a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai dangane da tabarbarewar harkokin tsaro a Jihar Kaduna.
Hon. Aminu ya ci gaba da cewa: “idan mun dawo a nan Jihar Kaduna, ko kuma na ce ma ka Arewacin Nijeriya, musamman Arewa maso yamma, Arewa maso Gabas da wasu sassan Arewa ta tsakiya, duk za ka taras lamarin kara tabarbarewa ya ke yi. Wasu sun dauki makamai sun shiga jeji da daddare su na shigowa kauyuka su na ta kashe mutane ba tare da wani dalili ba, domin lamarin kamar ma ba kudi ake nema ba, ana dai son a zubar da jini ne kawai a kuma kona dukiyoyin jama’a, wanda wannan babban abin tsoro ne.
A nan Jihar Kaduna kuma sai al’marin namu ya zama kamar ya kara muni, (Allah Ya sawwaka), fiye ma da sauran Jihohin. Domin kamar a Katsina ko a Zamfara, an san masu kai hari ne su ka kawo hari, an san in da suke za kuma a fuskance su a duk in da suke. Mu a nan Jihar Kaduna kamar yanda mai girma Gwamna ya yi jawabin yanda lamurran suke, abin yana da ban tsoro da ban firgicewa. Domin shigar da kabilanci, ko shigar da addini cikin al’amarin yana kara dagula shi ne, kasantuwar addini da kabilanci su na da tasiri a zukatan mutane, saboda haka idan ya cakuda da masu kashe mutane su na sace dukiyoyinsu, masu sace mutane su na karban kudin fansa ko lamarin ‘yan bindiga da makamantansu, sai lamarin ya kara kazanta. Wanda wannan kusan shi ne abin da ya ke neman zama a nan Jihar Kaduna, musamman kuma kudancin Kaduna.
Gwamna shi ne babban jami’in tsaro a cikin Jiha, domin shi ne ya dauki Alkur’ani ya yi rantsuwar zai kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jiharsa. Mun kuma yi imanin Gwamna yana yin bakin kokarinsa ba dare, ba rana. Kamar mu da muke majalisa da sauran shugabannin addini da shugabannin al’umma, ku ‘yan jaridu da duk wasu masu taimakawa, ya zama tilas mu hada hannu, mu hada kafa, mu hada zuciya, a hada hankali a fuskanci wannan masifar bakidaya domin a yi maganinta ta yanda kowa zai sami sukuni. Domin in aka bari ta kara tabarbarewa babu fa wanda zai zauna lafiya, babu wanda kuma zai sami sukuni.
Saboda haka abin da ya kamata mu yi shi ne mu gano bakin zaren kamar yanda Gwamna ya ce an kafa kwamitocin bincike da yawa, amma abin bakin cikin shi ne ba a aiki da sakamakon da kwamitocin binciken su ka gano ta hanyar hukunta wanda duk aka samu da aikata laifi, ko ma da har an je kotu ne ta yanke hukunci sai a sami wasu shugabannin siyasa su ce sun yafe wa wadannan da aka tabbatar da sun aikata laifin da ta jawo wannan masifar.
Gwamna ya yi alkawarin cewa shi ba hakan ba ne, zai bi sawun kwamitocin da aka kafa a gano bakin zaren, duk wadanda aka samu da laifi a kamo su a hukunta su, don maganin al’amarin. Na yi imani abin da ya kamata a yi kenan, na yi imanin Gwamna yana neman goyon baya da hadin kai a kan wannan al’amarin. Wajibinmu ne kuma mu ba shi hadin kai don mu gano bakin zaren, mu gujewa sanya son zuciya ko addini ko kabilanci don mu kara jagwalgwala lamarin. Wannan shi ne maganin wannan lamarin, matukar kuma ba hakan muka yi ba, lamarin nan kara lalacewa zai yi. In kuma ya lalace, to babu wanda zai tsira. Tilas ne a kira laifi, laifi, a kira masu aikata laifi, masu laifi, ba a kira su da sunan kabilarsu ba.

Exit mobile version