Connect with us

WASANNI

A Na Cigaba Da Tattaunawa Tsakanin Arsenal Da Thomas Partey

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana ci gaba da tattaunawa da wakilan dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Thomas Partey, wanda kungiyar take fatan saya da zarar an kammala kakar wasa ta bana.

Partey, dan asalin kasar Ghana yana shirin barin kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid kuma tuni aka bayyana cewa kungiyar Arsenal ta shirya biyan fam miliyan 44 domin sayan dan wasan ya koma kasar Ingila da buga wasa.

A kwanakin baya mahaifin dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Thomas Partey, ya bayyana cewa banda kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar Ingila akwai kungiyoyi da dama da suke bibiyar dan nasa wanda tauraruwarsa take haskawa a wannan lokacin.

Tuni aka bayyana cewa tattaunawa tayi nisa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da wakilan dan wasan akan irin albashin da zai dinga karba a kungiyar idan cinikin ya tabbata ya yinda Atletico Madrid take fatan Arsenal din ta biya fam miliyan 47 kamar yadda ta yiwa dan wasan farashi.

Itama kungiyar kwallon kafa ta PSG ta dade tana bibiyar dan wasan domin ya koma kungiyar a karshen kakar wasa sai dai bisa dukkan alamu abune mai wahala kungiyar ta samu damar daukar dan wasan dan asalin kasar Ghana.

Sakamakon matsalar tattalin arziki da kungiyoyi suka shiga saboda annobar cutar Korona, anyi zaton PSG zata samu damar doke Arsenal wajen sace zuciyar dan wasan musamman idan tayi masa tayin albashi mai tsoka sai dai Arsenal ma a wannan lokacin ta kokarta.

Tuni dai kungiyar Atletico Madrid ta bayyana cewa a shirye take data sayar da dan wasan idan har Arsenal ta amince za ta iya biyan abinda take bukata saboda kungiyar tana bukatar kudi musamman a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.

Kociyan Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana cewa kungiyar zata bawa duniya mamaki a kakar wasa mai zuwa musamman idan har ya samu irin ‘yan wasan da yake bukata duk da cewa kungiyar har yanzu tana da matsalar kudi.

A wannan kakar, Partey, ya buga wasanni 40 a kungiyar Atletico Madrid a gaba daya kofunan da kungiyar take bugawa kuma ya zura kwallo uku a raga sai dai banda Arsenal kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ma tana bibiyar dan wasan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: