Connect with us

TATTALIN ARZIKI

A Na Daukar Matakai Da Dama Wajen Ceto Tattalin Arziki

Published

on

Cutar Korona ta raunata tattalin arziki da takaita zirga-zirgan mutane da kasuwannin hannun jari a Duniya, yayin da dimbin mutane suka rasa rayuwarsu sakamakon wannan cuta. Masana sun bayyana cewa, akwai bukatar a magance wannan lamari. Bincike ya nuna cewa, cutar tafi yi wa mahimman fannin tattalin arziki barna kamar irin su man fetur da sha’anin zirga-zirga ta sama da sarrafa kayayyakin da ake amfani da su da fannin noma da dai sauran su.

A kwanan nan ne babban bankin Nijeriya (CBN) ta bayar da tallafi a cikin fannin harkokin noma, ta hanyar bullo da wasu mahimman shirye-shirye da zai inganta fannin. Shirye-shiryen ya bai wa manoman damar adana kudadensu. A cewar Daractan gudanarwa na CBN, Mista Isaac Okoroafor, sama da manoma miliyan 2.5 shuka amfana da shirye-shirye guda 17 wanda babban bankin ta samar domin inganta noma.

Haka kuma, gwamnan CBN, Gobernor Godwin Emefiele ya bayyana cewa, sun gudanar da wadannan shirye-shirye ne domin a tallafa wa fannin noma sakamakon rufe iyakokin kasar nan da aka yi saboda an bukatar a yi amfani da kayayyakin gida Nijeriya. Gwamnan babban bankin ya bayyana cewa, rufe iyakokin kasar nan ba karamin samun nasara aka yi ba ta bangaran tattalin arzikin Nijeriya.

Shahararren masanin tattalin arziki mai suna Mista Mike Osagie, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta karkata akalar tattalin arzikinta daga mai zuwa fannin noma, tun da dai farashin mai ya fadi a kasuwan Duniya. Ya bayyana cewa, kasar nan za ta fi amfana da fannin noma a yanzu fiye da man fetur. Osagie ya ce, mun koyi babban darasi lokacin da aka saka dokar takaita zirga-zarga, ya kamata gwamnatin da daura damarar magance dukkan mahimman fannuka kamar irin su fannin lafiya da na noma. Ya ce, ya kamata gwamnatin tarayya ta rungumi fannin noma domin wadata kasar nan da abinci da kuma samar da ayyukan yi.

Da ya ke jawabi a kan lamarin, Adetunji Ogunyemi, wanda shi masanin tattalin arziki ne kuma tsahon lauya mataimakin shugaban tsangana na fannin tarihi da ke jami’ar Obafemi Awolowo Unibersity, ya bayyana cewa, an samu mahimman darasi guda hudu a lokacin wannan cuta ta Korona a cikin kasar nan. A bangaren kasa gaba daya, Ogunyemi ya bayayyana cewa, Nijeriya ta samu kanta a cikin matsakancin hali a bangaren tattalin arziki da kuma fannin lafiya, sakamakon faruwar farashin danyen mai a kasuwan Duniya.

“Fannin tattalin arzikin da ya fi dacewa da Nijeriya shi ne fannin noma da masantarwa, wanda sai samar wa dimbin ‘yan kasa ayyukan yi, amma an yi watsi da wadannan fannoni shekara da shekaru a matsayin bangaren bunkasa tattalin arziki.”

Ya bayyana cewa, bangaren ‘yan kasuwa masu zaman kansu musamman ma bangaren sufuri da kananan ‘yan kasuwa wadanda suna da mahimmanci wajen inganta tattalin arzikin kasar nan, sun fuskanci babban darashi sakamakon cutar Korona. Ogunyemi ya ce, ya kamata gwamnatin tarayya ta rage yawan kudaden da take kashewa masu amfani tare da kashe su domin bunkasa fannonin tattalin arziki wadanda aka yi watsi da su.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: