Rabiu Ali Indabawa" />

A Na Matukar Asarar Amfanin Gona A Kasashen Afirka – AU

Tarayyar Afrika AU, ta bukaci kasashen Afrika da sauran hukumomin kasa da kasa na nahiyar, su hada karfi don magance matsalar asara da bata amfanin gona bayan girbi, domin tabbatar da wadatuwar abinci a nahiyar.
Tarayyar ta ce, nahiyar Afrika ce ta fi fuskantar matsalar karancin abinci a duniya, inda ta yi kiyasin 1 cikin mutane 4 a nahiyar na fama da karancin sinadaran gina jiki, ta alakanta matsalar da asarar amfanin gona mai yawa bayan girbi a kasashen dake fadin nahiyar.
Alkaluma daga AU sun nuna cewa, jimillar abin da ake asara a nahiyar ya kai sama da metric ton miliyan 100 a kowacce shekara, yayin da asarar da a ke a duniya baki daya, ya tsaya kan metric ton biliyan 1.3, kwatankwacin sama da kaso 30 na jimilar abincin da a ke samarwa domin amfanin bil‘adama, kana ta yi kiyasin yawan abincin da a ke asara a duniya, zai iya ciyar da mutane biliyan 1.6 a kowacce shekara.
Ta ce, wannan asarar na ta’azzara karancin abinci da yin mummunan tasiri kan muhalli ta hanyar lalata ban kasa da ruwa da kayayyakin gona da karfin da aka sa wajen samar da abincin da ba a yi amfani da shi ba.
AU ta jaddada cewa, asarar bayan girbi na rage kudin shigar manoma tare da ba da gudunmuwa ga hauhawar farashin kayayyakin abinci.
Kiran na rage asara da bata amfanin gona da Tarayyar ta yi, na zuwa ne gabanin taron bayan girbi da baje koli karo na 2 na nahiyar, da za a yi daga ranar 17 zuwa 20 ga wata, a hedkwatar AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.
Haka zalika rahoton na AU ya bayyana cewa, Jami’ar kungiyar tarayyar Afrika AU, ta yi barazanar cewa yanayin aikin gona a Afrika zai iya fuskantar gagarumar hasara sakamakon dumamar yanayin da ake fama da shi a duniya a sanadiyyar matsalar sauyin yanayi, sai dai idan har manoman nahiyar sun yi farar dabara ta hanyar aiwatar da dabarun noma na zamani wadanda zasu dace da sauyin yanayin.
Josefa Sacko, kwamishiniyar AU ta hukumar kula da tattalin arzikin karkara da aikin gona ta kungiyar tarayyar Afrika, ta yi wannan gargadi a lokacin taron tattaunawa game da samar da isashen abinci na Afrika wanda aka gadanar a Kigali, babban birnin Kasar Rwanda.
Ta ce, karuwar dumamar yanayin duniya, da karancin ruwan sama da ake fuskanta a sanadiyyar sauyin yanayin sun kasance a matsayin babbar barazana ga fannin aikin gona a Afrika, kasancewar mafi yawan manoman nahiyar har yanzu suna cigaba da gudanar da tsarin noman gargajiya.
Sacko ta ce, Afrika tana fuskantar matsananciyar barazana sakamakon matsalar sauyin yanayi fiye da sauran sassan duniya saboda yadda nahiyar ta dogara kacokan kan aikin gona a matsayin hanyar samun abinci.
A cewarta, akwai bukatar a samar da shirin hadin gwiwa tsakanin manoma, da masu tsara dabarun Shugabanci, da kungiyoyin raya cigaba, da shugabannin gwamnatocin Afrika domin aiwatar da salon aikin gona wanda zai dace da sauyin yanayin da ake fuskanta.

Exit mobile version