A duk shekara ana shigowa da tan miliyan 1.1 na albasa, duk da kasar nan ce ta biyu wajen noman albasa a Afirka a bayan kasar Masar.
Shugaba Kula da Hada-Hadar Kaauwancin Albasa na Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, Musatapha Khadiri, ya bayyana hakan.
Ya sanar da hakan ne a wajen taronsu da ya gudana a Sakkwato, inda ya kara da cewa, a kowace shekara Nijeriya na bukatar tan miliyan 2.5, amma tana noma tan miliyan 1.4 a shekara abin da ya kawo mata gibin sauran ke nan da ake shigowa da su.
A cewar Khadiri ya kara da cewa rufe kan iyakokin kasa da aka yi ya kara bunkasa noman albasa a Nijeriya, matakin da ya ce abin yabawa ne ga kasa don hakan zai sanya kasar ta dogara da kanta musamman a harkar noman albasa.
Ya ce, rufe iyaka a yanzu ya sanya manoma mayar da hankali ga noma don ciyar da kansu, amma duk da haka akwai ’yan wahalhalu ga ’yan kasuwar albasa na Afirka.
Shi kuwa Sakataren kungiyar Manoma da ’Yan Kasuwar Albasa ta Nijeriya, Aliyu Isah Mai Tasamu, ya ce da albasa za ta samu yanayi mai kyau za ta samar wa Nijeriya kudin shiga Dala miliyan 420.