Connect with us

KASASHEN WAJE

 A Na Zargin Shigar Da Gurbataccen Suga Kenya

Published

on

An kama wasu manyan jami’an gwamnatin kasar Kenya 10, bayan rashin tabbas a kan kyawun sikarin da ake shigar da shi kasar.

Daga cikinsu akwai shugaban hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki na kasar.

Kamen ya zo ne kwana guda bayan wasu manyan ministoci a kasar sun bayar da bayanai masu cin karo da juna a kan ko buhunhunan sikarin da aka kama wadanda aka shigo da su kasar daga Brazil na dauke da sinadarin mercury.

Ministan cikin gidan kasar ne ya bayar da umarnin kwace sigan, wanda ya zargi cewa ya na dauke da sinadarin mercury,bayanin da ya saba da na ministan ciniki da kasuwanci na kasar wanda ya ce sigan mai kyau ne ba shi da wata matsala.

A cikin ‘yan kwanakin nan, ana sa ido sosai a cikin harkar shigo da siga a kasar, inda aka kama ‘yan kasuwa da dama.

Babban Darakta a ma’aikatar cikin gidan kasar ta Kenya, ya bayyana gaban wani kwamiti a majalisar dokokin kasar, inda ya ce wasu daga cikin buhunhunan sikarin da aka shiga da su kasar na dauke da sinadarin dalma ba mercury.

A wasu sassa na kasar, farashin siga ya tashi saboda sa idon da ake yi wajen shigar da shi cikin kasar

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: