Zubairu T M Lawal" />

A Rika Hukunta Shugabannin Da Ke Nuna Wariya Da Kabilanci –Antonio Guterres

abinci

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin siyasa, da na Addini, da kuma sauran shugabanni a kan su daina yin kalaman wariya da nuna kiyayya ga wani bangare.

Babban Sakataren ya ce; irin wadannan kalaman na nuna wariya da kyama, ga launin fata ko kabilanci babu abin da yake haifarwa sai ya kawo rikici a cikin al’umma.

Sakatare ya kara da cewa,  don haka ya kamata a ba kowa hakinsa da ‘yancinsa, ba tare da tsangwama ba. Saboda kowane mutum yana da ‘yancin yin addininsa da kuma ‘yancin gudanar da addininsa a duk inda ya samu kansa.

Haka zalika mutum yana da yancin rayuwa a cikin kabilar da ba ta sa ba mautukar zai kiyaye dokokin yanayin zamantakewa.

Launin fata ko addini ko kabila ba zai hana mutum ya zauna a cikin jama’ar da ba ta su ba.

Babban Sakataren ya kara da cewa, “Don haka ne ma muke so kotuna su yi wata doka a kan irin wadannan kalaman na batanci, don ya zama an sami tabbatacen zaman lafiya.”

Saboda dokar za ta takawa shugabannin da ke nuna wariyar launin fata da masu nuna ra’ayin bambamcin addini da masu nuna kabilanci birki, idan doka za ta hukunta shugabannin da ke irin wanan dabi’ar to al’umma za su kiyaye dokokin nuna wariya.

Ya ci gaba da cewa, irin wadannan kalaman sun ja jawo asarar rayuka a duniya. Misali a  1994 yadda aka tsani ‘yan kabilar Tutsi da munanan kalamai da kisan gilla a kasar Ruwanda a shekaru 25 baya.

Wannan sakon dai wakilin sakataren majalisar Dinkin Duniya Mista Ronaldo Kayanja ne ya yi wannan jawabi a wajen wani taron gasa na ‘yan makaranta da ya gudana, a cibiyar yada labarai ta Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Legos a tarayyar Nijeriya.

Taron ya samu halartar dalibai daga makarantu daban-daban wanda hukumomi makarantun suka amince da wannan sakon na sakataren Majalisar Dinkin Duniya da ya janyo hankalin al’ummar duniya domin hadin kai da zaman lafiya.

Exit mobile version