Sabo Ahmad" />

A Sakonsa Na Sallah, Buhari Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya, Su Hada Kansu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kawar da daukkan bambancin da ke tsakaninsu, ta hanyar mutunta ra’ayi juna hada kai.

A sakonsa na sallah shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ai’ummar Musulmi su yi amfani da wannan lokaci wajen yin kyawawan ayyuka tare da zama wakilai nagari a duk inda suka samu kansu kamar yadda addinin Musulunci ya umarta.

Sannan ya tunatar da Musulmi cewa, lokacin sallah babba lokaci ne da ya kamata a tuna irin sadaukarwar da  Annabi Ibrahim Allaihis-Salam  ya yi da mika wuya bisa umarnin Allahto.

“Da irin wannan koyin ne muka sadaukar da kanmu musamman wajen tabbatar hakkin al’ummar da ba su da karfi, har ta kai ga, saboda haka ya zama wajibi mu sadaukar da kanmu domin wasu su amfana,”.

Misata Buhari ya ci gaba da bayyana cewa, addini hanya ce da take tarbiyyartan da dan’adam wajen yin ayyukan alheri.

Ya ce sai dai babban abin takaicin shi ne mutane da yawa sun bar koyarwar addini sun rungumi son zuciya da abubuwan ki , kamar cin-hanci da rashawa wadanda dukkan wadannan abubuwa addini ya yi hani da su.

Shugaban kasar ya kara karfafa manufar gwamnatinsa na yaki da cin hanci da karbar rashawa, wanda iata ce hanyar da za ta tsamo wannan kasar daga halin da ta fada da talauci  da tsadar kayayyaki da kuma rashin wadataccen abinci.

Ya ce ba za mu taba yarda da  mu bari ana ci gaba cin hanci  a kasar nab a, domin kuwa cin-hanci, al’amari ne da ke kasha kasa.

Kamar yadda y ace shi ne, ko da za a tsane ka a kan yaki da ci-hanci a matsayinka na shuga, dole ne ka tabbatar da ka ci gaba da wannan yaki har sai ka kawo karshen lamarin”

Dangane da batun kalubalen da wannan kasar ke fuskanta kan batun tattalin arzikin kasa kuwa, shugaban cewa ya yi, wannan al’amarin ya fara kawo karshe, domin kuwa akwai tsare-tsaren da wannan gwamnatin ta kawo wadanda za su kara bunkasa tattalin arzikin wannan kasa.

Exit mobile version