Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

A Shakara 50 Ba Za A Sake Samun Kamar Ronaldo Ba – Figo

by Muhammad
January 25, 2021
in WASANNI
3 min read
Figo
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tsohon dan wasan kasar Portugal da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Luis Figo, ya bayyana cewa nan gaba ba za a sake samun dan wasa mai hazaka kamar Cristiano Ronaldo ba sai bayan shekara 50.

Figo ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da manema labarai a babban birnin kasar ta Portugal wato Lisbon bayan da akayi masa tambaya akan dan wasa Ronaldo da kuma irin tarihin daya kafa a duniya duk da cewa har yanzu baiyi ritaya daga buga kwallo ba.

A daren ranar Larabar satin da ya gabata ne Cristiano Ronaldo ya ci kwallonsa ta 760 a duniya a wasan Super Coppa na kasar Italiya da Juventus ta samu nasara da ci 2-0 a kan kungiyar Napoli, abin da ya sake tada ikirarin cewa shi ne dan kwallon da ya fi saka kwallaye a raga a duniya sai dai akwai takaddama a kan waye ya fi cin kwallaye a duniyar har yanzu.

Idan muka kalli tarihi Ronaldo ya fara nuna bajinta, inda a matsayinsa na matashin dan wasa, ya ci wa tsohuwar kungiyarsa ta Sporting Lisbon kwallaye 5, sannan daga baya  ya koma Manchester United ya ci kwallaye 118, bugu da kari ya ci kwallaye 450 a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, sannan sai kwallaye 85 a Juventus, sai kuma guda 102 a tawagar kwallon kafar kasar sa ta Portugal.

Sai dai ana ci gaba da kokwanto a kan ko Ronaldo din ne ke kan gaba a harkar kwallon kafa gaba daya wajen yawan kwallaye, saboda ‘yan wasan Brazil Pele da Romario na ikirarin cewa sun ci sama da kwallaye dubu daya a rayuwarsu.

“za’ayi shekara 50 ba’a sake samun dan wasa kamar Ronaldo ba idan muka kalli matasan ‘yan wasan da akeyi yanzu a duniya amma bance duniya ba zata sake ganin dan wasa kamar Ronaldo ba sai dai wanda zaiyi abinda yayi tabbas za’a dade” in ji Figo

A watan da ya gabata, Lionel Messi ya zarta kwallaye 643 da aka amince da su a hukumance cewa Pele ya ci wa kungiya guda, amma ba tare da bata lokaci ba kungiyar Santos ta Brazil, wadda Pele ya yi wa wasa suka ce gwarzon dan kwallon da ya lashe kofin duniya har sau uku ya ci musu kwallaye dubu daya da 19 idan aka hada da wasannin sada zumunta.

Bayanin Pele a shafinsa na Instagrm na nuni da cewa shine ya fi kowa saka kwallaye a raga a harkar kwallon kafa a duniya, da kwallaye dubu daya da dari biyu da 83 sai dai kuma, idan wasanni da aka yi a hukumance ne abin la’akari, dan kasar Brazil din, wato Pele, yana bayan Josef Bican, wanda masana tarihin kwallon kafa suka yi ittifakin cewa ya ci kwallaye 805 a cikin wasanni 530 a tsakanin shekarun 1931 da 1955, inda ya buga wa kungiyoyi 6 da kuma kasashen Austria da Czechoslovakia.

Pele ya ci kwallaye tsakanin 757 da 767 a wasannin da ya yi a sana’arsa ta kwallon kafa da suka hada da 92 da ya ci wa kasarsa Brazil sannan an sanya shi a matsayin na uku a bayan wanda ya taimaka wa Brazil a gasar kofin Duniya ta shekarar 1994 mai kwallaye 772 Romario.

A shekarar 2007 Romario ya yi bikin kai wa kwallaye dubu daya, adadin da ya hada da kwallayen da ya ci tun yana matashin dan wasa da kuma wasannin sada zumunta da na karramawa.

Shi ko Messi, wanda shekarunsa 33 yana da kwallaye 719 wadanda ya ci wa Barcelona da Argentina kuma yana iya cimma ma wadanda ke gabansa kafin ya yi ritaya saboda har yanzu yana buga kwallo.

SendShareTweetShare
Previous Post

‘Yan Bindiga Sun Budewa Babban Oditan Jihar Bauchi Wuta

Next Post

Ya Auri Wacce Ta Yi Jika Da Shi Saboda Guje Wa Shiga Aikin Soja

RelatedPosts

Arteta

Arteta Ya Mayarwa Da Paul Merson Martani

by Muhammad
3 hours ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya mayarwa...

Tuchel

Kowane Wasa A Ingila Mai Wahala Ne –Thomas Tuchel

by Muhammad
3 hours ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel, ya bayyana...

Alaba

Real Madrid Tana Cigaba Ta Tattaunawa Da Alaba

by Muhammad
3 hours ago
0

Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa...

Next Post
Aikin Soja

Ya Auri Wacce Ta Yi Jika Da Shi Saboda Guje Wa Shiga Aikin Soja

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version