A U Gama Farm Ta Yaye Dalibai A Kan Kiyon Kaji Da Kyankyasa

Dalibai

Daga Alhussain Suleiman,

Kimanin dalibai 30 ne maza da mata AU GAMA FARM da ke unguwar Gama a karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, ta ya ye  wadanda suka samu horo da kuma kwarewa akan yadda ake kiyon Kaji da kyankyasa an gudanar da bikin yaye daliban ne a cibiyar koyar da sana’oin na A U Gama farm , inda ya samu halartar al’umma daga ciki da wajen jihar. Day a ke zantawa da manema labarai bayan kamala bikin ya ye daliban shugaban na AU GAMA FARM Alhaji Nasar Usman Gama, ya nuna farin cikin shi da aka samu nasaran yaye daliban karo na farko da suka samu  kwarewa akan kiyon Kaji da Kyankyasa wannan nasara ce babba da cibiyar koyar da sana’oin ta AU GAMA FARM ta samu .

Nasar Usman Gama sai ya hori daliban cewa su tabbatar sun yi amfani da kwarewar da suka samu  a cibiyar ta yadda nan gaba su ma za su koyar da wasu .Shugaban na A U GAMA ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da manya da kana nan yansiyasa da kuma shugaban karamar hukumar ta Nassarawa Hon. Auwalu Shu’aibu Aramposu wajen turo matasan yankin domin su koyi sana’oin dogaro da kai. Ya yin yaye daliban an taimaka masu da Kaji da kuma ba su shaidar kammala horon a suka samu daga AU GAMA FARM.

 

Exit mobile version