Hussaini Baba" />

A Wannan Shekarar Za A Fara Gina Filin Jirgin Sama A Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Hon. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya bayyana cewa, cikin wannan shekarar ta 2019 za a fara gina filin jirgin sama a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya bayyana haka ne yau a lokacin da tawagar Kamfanin da jihar za ta yi haxin gwiwar gina filin Jirgin saman suka kawo masa ziyara a muhallin da za a gina filin jirgin saman da ke Rawayya, Gusau.

Hon. Matawalle ya bayyana cewa, wannan ginin haxin gwiwa ne da Kamfanoni masu zaman kansu da gwamnatin Jihar. Za su gina don samun ci gaban jihar da bunqasa tattalin arzikin jihar.

Haka kuma gwamnan ya tabbatar wa al’ummar garin Rawayya cewa, da mutanensu za a yi aikin, kuma duk kayan aikin da kamfanonin za su yi aiki da su indai akwai shi a Zamfara, toh a nan za a saya.

A nasa jawabin, wakilin haxin gwiwar na Bankin Heritage kuma Daraktan bankin na Abuja, Mista Goge Oko Obah ya bayyana cewa, bankinsu ya saba gina filin jirgin sama a qasar nan, kuma da yardar Allah wannan na Zamfara cikin shekaru biyu za su kammala ginashi. “muna tabbatar wa da gwamanatin Jihar Zamfara cewa cikin shekaru biyu za mu gama aikin”.

Shi ma a nasa jawabin, wakilin kamfanin gina filin jirgin sama  na ‘Ulo Construction LTD.’ Mr Uche Oko Ponu ya tabbatar da cewa, za su gina filin jirgin sama na zamani, kuma ya xau alqawarin gina ma al’ummar da ke maqwabtaka da filin jirgin saman gina masu asibiti da Makaranta kyauta.

Tsohon babban jami’in banki, kuma shahararren xan kasuwa, Dakta Dauda Lawal dare (Gamjin Gusau) na xaya daga cikin jigogin haxin gwiwar gina filin jirgin saman. Dakta Dauda ya bayyana jin daxinsa ganin yadda al’ummar Jihar Zamfara za su samu filin jirgin sama na zamani a lokacin gwamna mai kishin al’umma Bello Matawallen Maradun. Gamjin Gusau Ya ce, “samar da filin jirgin sama zai fidda mu daga cikin wasu matsaloli da kuma bunqasa tattalin arziqin Jihar Zamfara.”

 

Exit mobile version