Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
A yau Alhamis ne Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ke jagorantar manyan jami’an gwamnati domin amsar allurar rigakafin Korona a bayyanar jama’a domin al’ummar jihar su rungumi rigakafin hannu biyu-biyu.
Hakan na zuwa ne bayan da jihar ta samu dozin -dozin 80,570 na rigakafin Korona daga cikin adadin dozin 150,000 da hukumar lafiya a matakin farko ta tarayya (NPHCDA) ta ware wa jihar a kokarinsu na tabbatar da kare jama’a daga kamuwa da cutar na Korona.
Mataimakin gwamnan jihar Bauchi Sanata Baba Tela shi ne ya sanar da hakan a jiya yayin da ke amsar rigakafin wanda aka adanasu a dakin sanyaya maguna da ke asibitin koyarwa na Jami’ar ATBUTH da ke jihar.
Ya ce, wannan rigakafi ne wanda aka tantance kuma kasashen duniya da dama su na amfani da shi a halin yanzu inda jihar ma ta shirya domin amfani da wannan rigakafin.
Ya ce, gwamnan jihar Bala Muhammad da kansa zai jagoranci tawagar manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki domin kaddamar da fara yin Rigakafin a zahirance a yau Alhamis domin jama’a su yi koyi gami da amsar rigakafin hannu biyu-biyu.
Sanata Tela wanda kuma shine Shugaban kwamitin karta kwana kan yaki da Korona da zazzabin Lassa a jihar, ya kara da cewa za a kai rigakafin dukkanin kananan hukumomin da suke jihar 20 da gundumomi 323 domin yi wa jama’a rigakafin a sauwake.
Ya nemi jama’a da su rungumi rigakafin ba tare da wani taraddidi ba domin ya bada tabbacin cewa Gwamnatin jihar a kowani lokaci muradinta shine kare rayuka da dukiyar jama’a gami da lafiyarsu, yana mai cewa rigakafin na da matukar amfani domin kare al’umma daga annobar ta Korona.
Tun da farko, Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar (BASPHCDA), Dakta Rilwanu Mohammed ya ce rigakafin ya iso jihar ne da yammacin ranar Talata inda kuma kai tsaye aka nufi dakin sanyaya maguna kamar yadda hukumar lafiya a matakin farko ta tarayya NPHCDA domin kiyaye sunadarin allurar.
Ya ce za su yi allurar rigakafin ne daidai da tsari da ka’idar da aka gindaya musu. Ya Kuma bada tabbacin cewa kowa zai samu rigakafin ba tare da shan wani wahala ba.
Rilwanu sai kuma ya ce sun kimtsa jami’ai da kayan aikin da za a gudanar da wannan rigakafin da su a sassan da suke jihar.