Sabo Ahmad" />

A Yi Murnar Cin Zabe Cikin Hankali—Barista Hadiza

Shugabar mata ta kungiyar manyan ma’aikatan jami’a ta kasa (SSANU) Barista Hadiza Kabir, ta yi kira ga al’ummar kasar nan, musamman matasa da cewa, bayan an bayyana sakamakon zabe, su yi murna cikin hankali da natsuwa yadda za su gama lafiya.
Kamar yadda ta ce, daman bisa dabi’a irin ta dan’dam, duk lokacin da wani abin farin ciki ya same shi yana yin murna, domin nuna jin dadinsa da godiyarsa ga Allah. Sai dai babban abin da ya kamata a kiyaye shi ne, kada wannan murnar ta kai ga wuce gona da iri.
Haka kuma ta nuna cewa, ya kamata abubuwan da suka faru na nuna murna a zaben shekara ta 2013, wanda wasu da yawan matasa suka rasu, wasu kuma suka ji raunuka sakamakon yin wauta da abin hawa, ya zama darasi a wannan karon yadda kar mu sake hakan ta sake faruwa.
Haka kuma ta kara da cewa, kada wajen yin murnar an ci zabe kuma a kai ga tonon wadanda suka fadi zabe, har ta kai ga an fusata su, yadda su ma za su iya mayar da martani, karshe hatsaniya ta faru, har kuma wani abu mara dadin ji ya biyo baya.
Da ta juya kan batun ‘yan takara kuwa, Barista ta ce, su ma suna da gudummowar da za su bayar wajen tabbatar da zaman lafiya a kasa. Gudummowar ta su kuwa, ita ce, da zarar sun tabbatar da cewa, ba su samu nasara ba, to su amince da hakan, kuma su taya wadanda suka samu nasarar murna tare da tabbatar da bayar da gudummowarsu wajen gina kasa.
Domin kuwa, abin ya kamata su fahimta shi ne, duk wanda ya tsaya takara akwai yiwuwar samun nasara ko faduwa, kuma duk wanda ya zo ya karbi sakamakon da hannu bibbiyu, a yi godiya ga Allah bisa abin da ya faru. Domin ta yiwu idan ba a samu nasarar cin zabe a wannan lokacin ba, ana iya samu a lokaci na gaba.
Haka, Barista ta yi kira da babbar murya musamman ga al’ummar Arewa, da su fito a zaben da za a yi na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi ranar Asabar 9, ga watan Maris, 2019.

Exit mobile version