A Zahirin Gaskiya Yawancin Faduwar Jarrabawa Laifin Dalibai Ne – Umar Saleh

Umar Saleh

Galibi ana samun wadanda suke kallon yawaitar faduwar jarrabawar wasu dalibai ga malamai saboda wasu dalilai nasu da suke ganin su ne gaskiya. Sai dai kuma, bakonmu na Duniyar Makarantu a wannan makon ya ce masu irin wannan tunanin su sake, domin idan an bi ta barawo a bi ta ma-bi sawu. Ko mene ne dalili? Ga tattaunawar:

 

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi?

Sunana Umar Saleh Muhammad sunan da aka fi sanina da shi shi ne Comr Umar Saleh Zara

 

Ko za ka fadawa masu karatu dan kaitaccen tarihinka?

Takaitaccen tarihi na shi ne, ni dai an haifeni a tsohon garin Zara da ke karamar hukumar kumbotoso a jihar Kano, na yi makarantar firamare a makarantar M. T Aulad Zara, bayan na kammala na tafi makarantar Sakandare me suna Dan Ladi Nasidi secondary school inda na tafi makarantar GSS Na’ibawa na kammala a can. Zuwa yanzu ina karatu a makarantar Kano State Polytechnic ina yin National Diploma bangaran Mass Communication.

 

Kafin ka kammala makarantar Sakandare wanne fanni (Course) ka fara sha’awar karanta?

To ai ni tun kafin na shiga makarantar firamare ba wani kwas da nake sha’awa kamar mass comm kuma har na shiga Sakandare na kammala shi dai kwas da nake sha’awa kenan.

 

Kafin ka kammala makarantar Sakandare wacce makaranta kake da burin shiga cikinta dan ci gaba da karatu?

Makarantar Bayaro Unibersity ita nake burin shiga amma kasancewa dana zana jarabawar JAMB makin da na samu 178 ne Ni kuma babu kwas din da nake mutukar so kamar mass comm shi kuma a Lokacin sai kana da maki 200 duk da zan iya samun wasu kwasis din da wannan makin amma na hakura na ce gwara na zo na yi national Diploma akan kwas din da na fi kauna.

 

Me ya ja hankalinka kake sha’awar kwas din?

Saboda na rinka taimakon mutane wajan isar da sakonsu da kuma taimakawa wajan hana ha’inci kuma na kawowa addinina da yanki na, ci gaba ta wannan hanyar saboda ko da ba komai zan samu alaka da kafafan yada labarai wanda ta nanne zan samu damar isar da sokonnin Al’umma abun da yake damunsu.

 

Ya batun Iyaye ko suna da buri akanka game da abinda suke son zaba maka na karatunka, wanne fanni suke son ka karanta?

A zahirin gaskiya in dai bangaran karatu ne iyayena sun bani dama a kan abin da nake so na ga ya yi min saboda kar su zabamin wanda bana so karatun ya zo bai musu yadda suke so ba kuma dama tun can sun san wanne kwas nake so don haka suma suka bani goyan baya akai.

 

Wanne irin gwagwarmaya ka sha wajen neman admission kafin ka samu?

Eh gaskiya an sha gwagwarmaya daga farko kafin a samu kasancewa ni ra’ayina na fi so na nema da kaina ya zama ba da wani aka hada ni da shi ba, domin ya yi min tsani amma dai daga karshe abun ya zamanto min me sauki kasancewa duk abun da ake nema na cika ka’ida ina da shi.

 

Ya batun cike-ciken form ya kasance?

Hahaha.. gaskiya cike-cike har kusan gajiya na yi da shi sakamakon wani abun ma sai na rasa kalmar da zan rubuta sai na tambaya saboda ina da karancin bocabulary.

 

Da su wa ka fara haduwa bayan shigarka makarantar da kake ciki a yanzu?

Alhamdu lillah bayan shiga ta makarantar na fara haduwa da mutane uku Jamil A . Uba Batakaye, Jafar Salisu kofar Mata, Khadija Musa Abdullahi su ne mutanen da na fara haduwa da su.

 

Ko za ka iya tuna sabbin abubuwan da ka fara cin karo da su cikin makarantar?

Sabbin abubuwan dai a gurina bai huce ganin mutane kabila daban-daban da kuma kowanne da irin al’adarsa da kuma shigarsa ba.

 

Kusa da wa ka fara zama a farkon shigarka aji?

Na zaunane a gurin wani me suna Tauhami Abdulkadir kasancewa na ganshi a set din farko ni kuma ina san zama a farko.

 

Ko za ka iya tuna darasin da aka fara yi muku a farkon shigarka aji?

Eh darasin da aka fara yi mana farko shi ne Introduction for mass communication.

 

Ya darasin ya kasance a wajenka musamman yadda a lokacin kake farkon fara shiga aji?

Gaskiya ni inda na dauki abun da zafi sosai da wahala da naje sai na ga abun bai kai haka ba saboda ana bayar da dama ayi tambayar abun da baka gane ba to da na yi tunanin kawai idan aka yi abu hucewa ake yi ba’a bayar da damar tambaya.

 

Ya zirga-zirgar zuwa makarantar ta kasance?

To Allahamdudillah kasancewar garinmu yana da dan nisa kafin makarantar dole sai na fito da wuri saboda kar na makara to wani lokacin kuma na rasa abun Hawa da wuri.

 

Wanne darasi ka fi so kuma me yasa ka ke sonsa?

Darasin da na fi so a yanzu shi ne broadcasting saboda shi ne ake koya mana yadda za ka yada labari da sauransu sai kuma Adbertising darisin da ke koyar da yadda ake tallata haja.

 

Wanne dalibi ne ko daliba ce ta fi birgeka cikin ajin, kuma me ya sa?

Su Uku ne sune su ka fi burgeni saboda ra’ayinmu ya zo iri daya wajan yin karatu su ne Jafar Salisu kofar Mata, Jamilu A. Uba Batakaye, Khadija Musa Abdullahi.

 

A bangaren malamai fa, wanne malami ne ko malama ce ta fi birgeka kuma me yasa?

Malam Salihu Suleh Khalid shi ne ya fi burgeni.

 

Mene ne burinka na gaba game da karatunka?

Burina shi ne na kammala wadda nake yi na dora da “degree”.

 

Wanne abu ne ya taba faruwa da kai cikin makarantar na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ka taba mantawa da shi ba?

Abun dai shi ne fitowar jarabawarmu ta farko kowa yana tsoran zuwa ya duba amma ni cikin ikon Allah da na yi kuru na duba sai na ga dukkan kwasis din A, B, C na samu babu kasa da haka, A lokacin lebal coodinetor din mu har murna ya tayani kuma ya ce ina cikin dalibai 12 wanda su ka fi kowa samun maki a ‘yan kilas din mu.

 

Kasancewar yanzu ka kwan biyu kana karatu cikin makarantar shin ya karatun yake tafiya, malaman suna yi muku yadda za ku fahimta ko kuwa dai kawai ana bin yarima a sha kida ne?

Ba abun da zan cewa malaman mu sai godiya kasancewar suna iya kokari wajan koya wa da kuma ganin kowa ya fuskanta har bayar da dama su ke mutum ya yi tambaya akan abun da bai gane ba na baya kafin a dora da darasin da za a yi a ranar, Illa iyaka dai kalubalan shi ne ya jin aikin da kungiyar malaman kwalejojin fasaha take yi a yanzu wanda sun kusa sati 7 suna yi shi ne kawai ya kawo nakasu.

 

Ya batun matsalar kari oba da wasu daliban ke dauka ko da yaushe me za ka iya cewa akan hakan?

Na yi duba sosai tun farkon fitowar jarabawarmu ta farko a zahirin gaskiya yawanci laifin daliban ne kasancewa wasu basa zuwa makarantar sosai kuma ba sa dagewa da karanta abun da aka koya musu, saboda san jiki da ganda wanima sai ki ga saura sati 1 a fara jarabawa sannan ya ke tambayar handout da sauran kayan karatu ya je ya duba, wasu kuma kwata kwata ba sa karatu sai Lokacin jarabawa sannan suna zabar wani abu ne daga cikin abun da aka yi musu su karanta ba sa karantawa gaba daya to idan aka samu matsala ba a yi tambaya a inda su ka karanta ba Kinga babu abun da za su iya amsawa, sannan wasu kuma hadda su ke yi idan aka samu matsala ta kwace kinga kenan babu abin daz a su iya rubutawa tun da ba fahimta su ka yi ba kawai hadda ce.

 

Ya kake kallon yadda karatu ya ke tafiya a yanzu?

A zahirin gaskiya yadda karatu yake tafiya akwai bukatar a tsaya ayi gyara kasancewa za ki ga dalibai cunkus a aji babu wadatatun ajujuwan da za a rabasu domin kowa ya yi karatu cikin sauki. Sannan akwai bukatar ace an samar da duk abubuwan da ake bukata na koyo da koyarwar a makarantu kamar irin na’ura me kwakwalwa da guraran da mutum zai je ya yi bincike da dai sauransu. Uwa Uba matsalar yajin aiki wanda Babbar matsala ce yanzu fa idan mutum ya shiga makaranta ba shi da wani lokaci da zai ce zai fita har sai ya ga ya fita din, saboda ko da yaushe ka iya shiga ya jin aiki sai kiga wanda zai yi shekara 2 ya kammala ya yi shekara 3 ko 4 ko kiga mutum ya yi shekara 2 a aji daya saboda yajin aiki.

 

Wanne kira za kai ga gwamnati game da ci gaban karatu?

Kiran dai shi ne dan Allah a daina bari malamai suna tafiya yajin aiki hakan ba karamin koma baya ya ke kawowa ba ta fannin ilimi a inganta makarantu ta hanyar samar da kayan koyo da koyarwar a samar da ajujuwan wadadatatu.

 

Ko kana da wani kira da za kai ga su malaman makaranta game da dalibai?

Kirana anan shi ne bai huce na ce su ci gaba da hakuri ganin yadda cewa wani dalibin idan ya yi wani abun sai ka ji hatta kai dalibin ma ya baka haushi to su ci gaba da hakuri su dauki dalibai kamar ‘ya’yansu da kannansu su sa ni cewa ladan da za su samu ba iya na duniya ba ne har da lahira.

 

Wanne shawara za ka bawa sauran dalibai masu kokarin shiga makarantun jami’o’in da kwaleji?

Shawarar dai ita ce su cire wasa a ransu su mai da hankali wajan yin abun da ya kawo su.

 

Ya batun da ake fada na game da irin shigar da ‘Ya’Yan hausawa ke yi a ire-iren makarantu irin haka, za su sako kayan mutunci daga gida ya yin da suka fito waje sai su canja su shiga cikin makaranta da wata shigar daban, shin ya abin ya ke?

Gaskiya ne hakan tana faruwa saboda wani Lokacin sai ki kasa gane ‘ya’yan hausawa da kuma ‘ya’yan wasu yaran daban, amma ni dai a bangaran da nake kamar haka ta ragu sosai inda na lura dai duk da ba tsayawa nake yi domin yin buncike akan batun ba.

 

Idan ka ci karo da masu irin wannan shigar ya ka ke ji a zuciyarka?

Gaskiya bana jin dadi a zuciyata saboda kawai sai na ji kunya ta kamani bama na tsayawa na kallesu kar su yi tunaninin cewa hakan da su ka yi sun burgeni.

 

Wacce irin shawara za ka bawa masu irin wannan shigar?

Shawarar da zan ba su shi ne su ji tsoran Allah su daina su sa ni hakan ba abu ne me kyau ba kuma shigar tasabawa addini da al’adarsu.

 

Toh ya batun soyayya fa ko akwai wadda ta taba kwanta maka a rai cikin makarantar da har ta kai kun fara soyayya da ita?

Hhhhh babu sai wacce take taimakamin tare da kara karfin gwiwa wajan karatu da yin buncike duk abun da ban saniba tana warwaremin itama haka ita ce dai Khadija Musa Abdullahi.

 

Wacce irin mace ka ke so?

Hmmm me ilimin addini da na zamani da kuma ibada da tsoran Allah.

 

Misali ace ka yi aure yarinyarka ta girma ta gama makarantar sakandare, shin za ka iya barinta ta ci gaba da karatu har zuwa jami’a?

Sosai ma kuwa har gaba da Jami’a idan da akwai zan iya barinta in dai tana so.

 

Mene ne burinka na gaba game da karatunka?

Burina shi ne na kammala wacce na ke yi na dora da degree.

 

Yanzu saura shekara nawa ka kammala makarantar?

Saura shekara daya insha Allah da ba dan annobar Corona ba da kuma yajin aiki da ake ta yi da tuni a wannan Shekarar zuwa bayan babbar sallah zan kammala.

 

Wanne irin abinci ka fi so da abin sha?

Abinci na fi son shinkafa da miya, abin sha kuma Zobo me sanyi.

 

Me za ka ce da makaranta wannan shafi na Duniyar Makarantu?

Hakika Ina matukar godiya sannan ina jinjina wannan shafi sakamakon yadda yake kokari wajan zantawa da dalibai daban-daban wanda hakan yana kara musu karfin gwiwa sosai. Hakan ba karamin abububawa ne sannan ina jinjina miki ke kanki me gabatarwar ganin yadda kike jurewa tare da tambayoyi wanda za su zaburar da mutum tare da ganin komai ya tafi dai-dai ina godiya sosai gaskiya.

 

Me za ka ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP?

To Allahamdudillah hakika Jaridar LEADERSHIP ta zama bango a garemu wanda muke dafawa domin isar da sakon mu inda muryoyinmu ba za su kai ba domin Jarida ce da zan iya cewa ba mu da kamarta wanda ta tara kwararrun ma’aikata masu iya ma’amala domin ganin an kawo ci gaba abubuwan ba za su lissafu ba sai dai na yi mata addu’ar samun daukarkar ta huce ko wacce Jarida a fadin kasarnan dama duniya baki daya ita da ma’aikatanta.

 

Ko kana da wadanda za ka gaisar?

Kwarai kuwa farko dai ina gaida mahaifiyata Malam Fatima Saleh Muhammad Zara da kuma yayana Abubakar Sale Zara, yayata Malama Yahanasu Saleh Zara, Amina Saleh Zara,Rukayyatu Abdullahi, Tasiu Ya’u Usman, Ibrahim Saminu ‘Yankatsari Jamilu A Uba Batakaye, Jafar Salisu kofar Mata, Sani Tahir, Khadija Musa Abdullahi Fatima Zara Adamawa.

 

Muna godiya Malam Umar Sale

Ni ma na gode.

Exit mobile version