Yusuf Shuaibu" />

Abbuwan Da Za Ka Duba Wajen Zabe ‘Yar Dattawa Lokacin Aure

Daga abubuwan da muka saba ambata yayin zaben abokiyar zaman, akwai ‘yar gidan dattawa”. Watakila saboda mun fahimci cewa ba ango da amarya ne kadai suke da rawar takawa a cikin zamantakewar aure ba. Jama’a da dama ma suna ganin iyaye su ne suke samar da ainishin shimfidar da za a yi baje-kolin duk abubuwan da ka iya faruwa tun daga farkon al’amari har zuwa karshe. Sai dai mutane da dama suna ganin, sunan ne kawai ya zauna a bakunanmu. Amma idan aka ce mu ware su daga ‘ya’yan gama garin mutane, sai wankin hula ya kai mu dare. Amma watakila za mu iya saurin fahimtar wace ce ‘yar dattawa kawai idan mun yi wa kanmu tambayoyi a kalla guda uku. Wato sai mun san wane ne Dattijo, mun kuma san wace ce ubanta ya zama dattijo a wurin ta. Sannan wace ce ‘ya a wurin babanta? Ba mamaki ka ji gabobin bambarakwai ko ma gingiringim kafin mu tisa su.

  1. Wane Dattijo?

Idan maganar zaman aure kake yi, ba bukatar sai ka tattaro kalmomi sittin ko saba’in, don bayyana suffofi ko kamannin Dattijo. A saukake, Dattijo shi ne wanda ya sami daraja da kima a idanu da zukatan ahalin gidansa. Ta hanyar kula da hakkoki da kyautata musu da kuma kare mutumcinsu da nasa a idanun sauran al’umma. Wannan tsirarun kalamai sun isar maka, kuma mai sauraron ka zai iya fahimtar ka, cikin sauki.

Za mu iya fahimtar abubuwa muhimmai a cikin wadannan jumloli guda biyu. Na farko za mu iya ganin ainihin dattakon yana farawa ne daga cikin gida. Wato kenan, lamarin ba ya ta’allaka a kan mu’amularsa ta waje ba ce kawai. Ka iya cewa ma ta gidan ce a’ala. Watakila ka ce, me ya sa sai dattijo ya sami daraja a gidansa? Wannan tambayar kuma ita za ta ba mu damar fito da sauran gabobin da mu ka yi alwashin bayyanawa.

 

  1. Wace Ubanta Ya Zama Dattijo A Wurinta?

Sau da yawa kake iske mutumin da ake darajawa da ganin kimarsa a gari, irin mutumin da kai tsaye ma idan an ce ka nuna dattijo za ka iya nuna shi. Amma idan ka shiga cikin gidansa sai ka taras ba shi da ko kwatar wannan daraja. Ba kuma wai a wurin matansa kadai ba, har a wurin wasu daga yaransa.  Wannan na iya zama saboda dalilai daban-daban. Watakila hanyar da uwa ta dora su a kai kenan, saboda wani buri ko manufa nata. Musamman saboda rashin kyautata mata da yake yi. Ko kuma dai shi ne ya bayar da wata baraka, ta hanyar kasa adalci tsakanin iyayen ko su kamsu ‘ya’yan.  Domin a yanzu abu ne da ya zama tamkar ruwan dare, samun iyaye mazan da kansu kawai su ka sani. Ba ruwan su da bukatu ko maslahar yaransu. Hakan yakan iya bayyana a wasu gidaje, kuma karara yaran suna gani kuma sun fahimta. A irin wannan gida babu abin da zai hana kimar uba zubewa. Da sauran dalilai masu kama da wadannan, wadanda lallai bayyanar su takan haddasa raini.

Duk ma dai wanda ya faru daga wadannan dalilai, sau da dama za ka taras ya sanya kokonto game da kimar uba a zuciyar yaransa. Kuma idan ba a dau mataki ba, wato shi uba bai zauna da yaransa ya wayar musu da kai ba, ko kuma ya yi wasu ayyukan da za su kashe kaifin waccan badakalar ba. Sai ka taras a hankali darajarsa tana zubewa a idon yaransa. Zargi da munanan zato su na maye zukatansu. Akwai kuma wanda dama can uban ba mai dattakun ba ne, a cikin mu’amularsa da mutanen waje da su na gidan. To ko ma dai me ya faru, idan ka hadu da wanda a wurinta mahaifinta ba dattijo ba ne, in dai kun saba sosai, za ka iya fahimtar irin kallon da take yi masa to ka jingine ta a gefe guda tukun. Domin ba ita muke  nema ba. Wanda muke nema a nan ita ce wanda Allah ya makantar da idonta game da kallon dukkannin wasu aibu ko munanan halaye na mahaifinta. Har ma take yi mar kallon wani mutum mai mutumci kuma abin alfarin wanda ya dangantu da shi.

Wace ‘Ya A Wurin Babanta?

Idan a gwarance za ka amsa tambayar, watakila ka yi tunanin magana ake ta wanda ba a shakka game da cewa ‘ya ce ta halak-malak a wurin mahaifinta. Wanda ba a mata zargin wani abu, amma a azance, idan an ce mutum dan babansa ne, akwai dalilin fadin hakan. Kai daga ji ka san ba waccan maganar ta gwari-gwarin ake ba, maganar azancin ake yi. Kenan ana cewa mutum dan babansa ne yayin da ake so a nuna ya gado wasu dabi’u irin na mahaifin. Ko tsabar kamanni da suke yi a surar jiki da motsinsu. Da abubuwan da su ka yi kama da wannan. Haka nan kuma za a iya kiran sa hakan saboda yadda yake matukar alfahari da tunkaho da mahaifinsa. Amma koma bayan wadannan kai da kanka in ka fada musu za ka ji bambarakwai. Ba za ka taba ganin ‘ya mace ta dage a kan tafiya bisa wata dabi’a ko magana ko wani yanayin motsi irin na mahaifinta, ta yadda har mutanen da ke kusa da ita za su iya fahimtar hakan ba, face sai in tana kallon sa a matsayin mutum mai girman daraja kwarai. Amma a al’ada irin ta mace idan ba ta ganin kimarka ba ruwanta, ba za ta taba yin wani abu da zai sa a danganta ta da kai ba. Amma idan ka ga ana danganta wasu kamanninta da na mutum tana jin dadi, ko kuma ita da kanta tana danganta kamannin ko motsinta da ma mutum. To babu shakka ba karamar kima yake da ita a wurinta ba.

Kammalawa; Bayan kawo wadancan bayanai da su ka gabata, a nan ya kamata ka dauki dunkulallen sakon, wato da farko hikimar mutum ya zama dattijo a gida kuma dattijo a waje. Wato a kalla hakan zai taimaka wurin in ya yi magana a gidan, abin da ya zartar zai sami hadin kai. Kuma kai ma da kake a waje, in ya shiga maganar da ta shafe ka, zai yi ma adalci. Sannan idan ka waiwayi ‘yar da ta dauki mahaifinta a matsayin dattijo, da wanda ta zama ‘yar babanta. Za ka taras akwai muhimman abubuwa da suke tasiri a tunaninsu. Wadanda kuma su ne za su taimake su da mazajensu yayin zamantakewar auren. Wato yayin da mace ta taso ta ga mahaifinta tsayayye a kan al’amuransu. Yana kulawa da kare martabarsu dai-dai gwargwado. Abin da za ta tashi da shi a ranta shi ne, namiji shi ne abin dogaro, kuma mafi cancanta da girmamawa. Sabanin wanda za ta tashi ta taras sam ba ruwansa da wasu hakkoki nasu kansa kawai ya sani. Wanda za ta tashi tana yi wa maza kallon mugaye masu danne hakki da son kai. Kamar kuma yadda yayin da uba ya kasance mai nuna so da jan ‘yarsa a jiki. Za ta rika ganin namiji a matsayin mai masoyi kuma abin a so. Haka nan kuma wanda uba ya banzatar da ita, ya nuna ita ba abar so ba ce, za ta iya tashi da tunanin namiji ba abin so har zuci ba ne, tunda shi ma ba ya so, sai ko don wata bukatarsa.

Idan muka bi wannan rubutu, za mu banbance diyar dattajo da kuma wanda ba diyar dattijo ba. daganan zai mu ga irin abubuwan da za mu duba wajen zaben abokiyar zamantakewa idan mun tashi yin aure. Daga karshe sai mu ci gaba da addu’a, Allah ya yi mana zabi mafi alheri, amin.

Exit mobile version