Abdullahi Wuse Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Neja

’Yan majalisar dokokin Neja sun zabi Hon. Abdullahi Bawa Wuse a matsayin sabon shugaban majalisar, zaben da bai samu tarnaki ba kusan dukkanin ‘yan majalisar sun amince da zaben. Ya yin da Hon. Bako Kasim Alfa ya zama mataimakin shugaban daga karamar hukumar Bida, dukkanin su dai sabbin ‘yan majalisa ne a wannan zangon na tara.

Hon. Musa Sulaiman Nasko ya zama shugaban masu rinjaye daga karamar hukumar Magama, mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar kuwa gun Hon. Jagaba Danjuma Andrew, sai Hon. Musa Idris Batsa ya zama mai tsawatarwa a majalisar. Hon. Isah Dandodo daga karamar hukumar Rijau ya zama mataimakinsa.

Hon. Abdullahi Bawa Wuse tsohon shugaban karamar hukumar Tafa, kuma tsohon kwamishinan shari’a a lokacin mulkin Dakta Mu’azu Babangida Aliyu a jam’iyyar PDP da ya canja sheka zuwa APC kuma zababben dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Tafa, lauya ne masani shari’a wanda tsohon shugaban majalisar a zango ta takwas, Hon. Ahmed Marafa Guni ya zabo a matsayin wanda zai gaje shi.

Exit mobile version