Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja
Matashin nan ɗan Nijeriya, wanda ya yi yunƙurin tayar da bom a cikin a garin Detroit da ke Amurka shekarun baya, Umar Farouk Abdulmutallab, ya gurfanar da gwamnatin Amurka a gaban kuliya ya na mai zargin ta da tauye ma sa haƙƙi.
Abdulmutallab ya na zargin sashen shari’a na ƙasar ne da tauye ma sa haƙƙin bayyana addininsa ne.
Shi dai matashin ya na gidan yari ne a Amurka bayan da kotu ta yanke ma sa hukunce-hukuncen ɗaurin rai da rai daban-daban bayan da ta kama shi da laifuka kan yunƙurin tayar da bom ranar Kirsimeti a shekarar 2009.