Connect with us

ADON GARI

Abin Alfahari Ne A Ba Mu Masu Lillibi Damar Wakiltar ‘Yan’uwanmu A Majalisa  – Amina BB Farouk

Published

on

Barista Hajiya Amina Ummalkhairi Ibrahim BB Farouk ‘ya ce ga Marigayi Alhaji Ibarahim BB Farouk wanda ya yi Mataimakin Gwamnan Kano a shekarun baya. Barista gogaggiyar ma’aikaciya ce a gida da wajan Nijeriya. Ta shahara ne a fannin kula da ‘yan gudun hijira  da kuma jinkan Dan Adam wanda ta yi karatu mai zurfi a kai. Wakilinmu MUSTAPHA IBARAHIM KANO ya zanta da ita kamar haka:

Abun da za mu fara da shi shi ne sunanki da kuma takaitaccen tarihinki…

To ni dai sunana shi ne Barista Amina Ummalkhairi Ibrahim BB Farouk kuma a nan Kano na fara  karatu a faramare ta stelios daga nan na yi shekara biyu sai mahaifinmu ya mai da mu ni da kannena Makarantar Firamare ta Shahuci to daga nan kuma sai na shiga Makarantar Yan Mata ta Shekara bayan nan ne kuma sai na tafi Makarantar Sakandare ta Stelios daga nan ne sai Jami’ar Bayero B.U.K Kano inda na karanta harkar Shari’a bayan na yi Karatun da ake kira School for General Study da turanci wato kamar karataun share fage kenan a Jami’a sai na zo na yi karatun English da Islamic Low a B.U.K a tsawon shekara hudu bayan na yi bautar kasa

NYSC a Mani. to amma banje Low School ba a wannan lokacin saboda ina da wani yaro wanda yake da lalura sai natsaya na lura da shi da kuma sauran yara suka danyi wayo saina zo na yi Jarrabawa ta Low School a 1989.

Bayan nan kuma sai na kama aiki a Legas da yake a can maigidana yake aiki to ganin yadda rayuwar Lagos ta ke da wuyar al’amari musamman bangaran kula da Yara da tarbiyarsu sai na hakura da aikin da nake yi a Necon Insurance sai na zo na bude Ofishi na kaina kasancewata Lauya da ake kira AU Ibrahim & CO wanda in na samu aiki sai na tura ma’aikatana suje su gabatar da abubuwan da ya kamata Ni kuma ina cigaba da kula da Yara to iya aikin da nayi kenan a Lagos. Daga Lagos muka dawo Abuja Ni da mai gida na.

To kuma bayan nan ne sai na samu tafiya Ingila domin yin Karatun Mastas Digiri inda nayi karatu akan kula da Hakkin Dan Adam a can Ingilan kenan to kuma bayan na gama sai na kama aiki a bangaran lura da Yan gudun Hijira dai-dai lokacin da ake Yakin Iraki, a wannan lokacin na Yan gudun Hijira na Iraki da na Sumaliya suna shigowa to haka dai na zauna a Ingila na tsawon lokaci.

To daga nan ne kuma sai na dawo Nijeriya na kama aiki a Hukumar kula da Hakkin Dan Adam wato National Human Right Commission inda aka bani Babbar Jami’a mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma inda Ofishi na yake nan Kano.

To bayan nan kuma sai na dawo Hukumar kula da Tsare-tsare ta Kasa wato National Planning inda na shekara Bakwai ina aiki a wannan Hukuma. Kasancewa na fi ido kuma na fi sabawa da abinda ya shafi Hakkin Dan Adam akan wasu abubuwan to daga nan ne kuma sai na dawo Hukumar kula da Yan gudun Hijira ta Nijeriya wato National Refuges ko kuma IDP a takaice to kuma a nan na dade ina aiki domin na kai har abinda ake kira Mataimakiyar Darakta a wannan Hukuma ta Yan gudun Hijira ina wannan Hukumar ne kuma har wannan abu mara dadi na Boko Haram ya zo saboda haka za ka ga akwai Yan dugun hijira na cikin gida da kuma na waje suna zuwa zan iya cema dai wannan shi ne aikin da nayi a takaice kaji. Abun da bazan manta ba a wannan aiki shi ne irin wata addu`a da wata mace tayi mani na sanya albarka bayan mun basu tallafin kayan sana`a a matsayinta na mai `ya`ya tara (9) matar, ta ce da kaina nake so sai mu rike kawai muce mun bayar, amma gashi mu kawo musu zasu amfana da `ya`yan su.

 

Kafin mu cigaba, kin ce Ibrahim BB Farouk ne mahaifinki wanda na sani ya yi mataimakin Gwamnan Kano da Shata ya yi ma waka kenan?

E, shi ne mahaifina.

 

BB Faruku na Allah ke nan?

E, shi fa.

 

Kasancewar Mahaifinki Dan Siyasa ne har ya kai ga mukamin Mataimakin Gwamnan Kano, a matsayinki na gogaggiyar ma’aikaciya wacce ta yi aiki a gida da kasashen Turai musamman Ingila, ko kina da muradin gadonsa a harkar Siyasa?

Ba shakka ina so in gaje shi ba ma a harkar Siyasa ba a harkar komai ma domin wani abu da na ke alfahari ko kuma muke alfahari mu ‘ya’yansa kasancewar ba ni kadai ba ce ‘yarsa muna da yawa amma abin da yafi ban sha’awa a harkata ta aiki da Makaranta da sauran dai mu’amala na Jama’a dana fadi suna na cewa Amina Ummalkhairi Ibrahim BB Farouk sai ka ga Jama’a sun rufe ni suna cewa ke ce ‘yar gidan Malam? sai na ce E, ni ce saboda da yawa mutane suna kiranshi Malam ne kawai kasancearsa tsohon Malamin Makaranta kafin ma ya shiga siyasa to kuma irin karramani da girmamani ko girmamamu da akewa Iyalan Mahaifinmu Malam Ibrahim BB Farouk wannan ta sa inaso in gaje shi a komai domin siyasar sa ma ba ta tara abin duniya ba ce, hakan ce ma ta sa duk inda Dalibansako abokan siyasar suka gan mu sai sun masa Addu’a Allah ya ji kan Malam to ka ga Ni a fahimta ta mai wannan lamari na suna ba karamin mutum ba ne, to kuma a hakan Allah ya rufa mana asiri na al’amuran Rayuwa Alhamdulillah.

 

To shi dai kin ga a tarihinsa na siyasa ban da na malanta ya kai matsayin mataimakin Gwamnan Kano, Barista Amina Ummalkhairi wannan matsayi kike so ki hau a siyasance?

To a gaskiya ni a matsayina na Matar Aure kuma Musulma wacce na lura Mata masu daura Gwaggwaro ko kuma wani abu wanda ya kasa haka yawanci su su ke wakiltarmu a wurare da kuma magana da yawunmu kuma sau da yawa suna shaci fade ne kawai ba su san hakikanin matsalolinmu ba, to shi ne ya sa abin da nafi sha’awa kuma na ga yafi masalaha a al’adarmu da addininmu shi ne wakilci, domin wakilci daban shugabanci daban tunda an ce mata ba sa shugabanci amma dai ni ban ga inda aka ce mata ba sa wakilci ba amma idan da inda aka ce mata ba sa wakilci, to Jama’a ku gafar ce ni a kan wannan magana ta wakilci.

To Saboda wannan dalili ne abinda nafi sha’awa a mukaman siyasa shi ne zama na wakilci Mazabata ta Gezawea da Gabasawa a Majalisar wakilai ta Abuja daga Kano domin ta haka ne zan bada gudunmawata domin sauke nauyi na Ilimi da Lafiya da dama da Allah ya bani domin ka da kaje Lahira Allah ya tambaye ni wanna kokari na yi wajan taimakawa Jama’a a damar da Allah ya bani na fidda Jama’a da ga matsalolin da suke ciki na rashin kayayyakin more Rayuwa da kuma matsalar rashin ingantaccen kiwan lafiya da Ilimi da Al’ummar garin da Mahaifina yafi so a Duniya wato Gezawa da ake mata kirari da Geza kanwar Birni amma kuma in ka je za ka ga ba haka ba ne. To wannan dalili ne ya sa na ke son siyasa irin ta mahaifina domin fitar da al’ummata daga kangin da suke ciki na rashin ingantaccen wakilci, kuma kasan duk gudunmawar da zaka bayar yanzu da wahala ta fi ta wakilcin siyasa a yau.

 

Kasancewar kin yi aiki a Ingila, me kika koyo wanda in kin samu dama za ki aiwatar a nan kasar musamman ta fuskar siyasa?

To kasan mu siyasar mu ta Amerika muke yi ba ta Ingila ba kuma su wadanda suka dauko irin ta Amerika suma suna da dalili da suke ganin tafi da cewa da wannan kasar amma abin da nake so ka sani cewa abinda na fadama a baya na yi aiki na lura da ‘Yan gudun hijira a can amma su ma za ka ga da mutum ya zo an karbi bayanansa to shikenan za ka ga yana da damar zama kamar yadda yakamata kuma hakance za ta sa gurin zama kuma a sashi a hanyar da zai dogara da kansa ta yadda ba zai zama dan maulaba, kuma yana da ‘Yanci na ya yi korafi akan abinda yake ganin an mai ba dai dai ba, dan gudun hijira kenan a Ingila !!!

To kuma zaka ga Ministocinsu musamman ‘Yan Majalisu akwai wani abu da ake kira Surgery amma ba na Tiyatar Asibiti ba wanca likitoci ke yi ba a’a shi Surgery a Siyasar Ingila shi ne dole ‘Yan Majalisa su zauna da Mutanan su su san matsalolin su kuma su bude Ofisoshi da Ma’aikata ta yadda ko wacce irin matsala mutanan su suke ciki za su kawowa Dan Majalisa domin ya magance matsalolinsu da korafinsu in har da shi, to ka ga kuwa a nan ba haka abin yake ba a nan sai ‘Yan Majalisa sun ga dama suke shiga Mazabunsu to wannan yana damuna musamman in akayi la’akari da yadda mutanan mu suke rayuwa wanda Ni in na samu dama abune da nake ganin ko ba a samu Jama’a a yankunan Karkara ba to ya kamata a samu ko bangare daya ne na sashin koyarwa daya ne a wannan yanki domin ya zama an rage wa matasa maza da mata shiga Birane karatu kuma wannan abune mai sauki ko ta hanyar Kungiyoyin jin kai zaka ciyar da mutanan ka gaba ta hanyar da Doka ta yarda kuma ta amince amma rashin sani yasa mutane basa ma neman taimako daga Kungiyoyin waje yadda yakamata.

 

To karshe dai nasan akwai kalubale mai yawa musamman a bangaren bada dama ga Mata a Siyasa wanna kira za ki yi ga al’umma kasar nan?

To kamar yadda na gaya ma ne a baya mu masu yin lillibi ko daura dan kwali ko Hijabi abin alfahari ne a ce an bamu dama mun wakilci ‘Yan uwan mu Mata da muke da Al’ada da Addini iri daya, to mu ne ya kamata mu wakilci ‘Yan uwan mu da muka san su suka san mu yadda za mu yi wakilci dai-dai, ba a rika magana da yawunmu ba, cuta daban magani daban wannan ba dai-dai bane, kuma ina sane da cewa mafi alherin mutane shi ne mafi kyautata musu wannan shi ne Mahaifina ya koyar da ni wanann Hadisi tun ina karamar yarinya har kuma yanzu da nake da ‘Ya’ya da Jikoki a kan haka nake. Kuma Babban burina shi ne in gaji mahaifina a Siyasa da komai kuma in zama wakiliyar Gezawa da Gabasawa a Majalisar wakilai ta Abuja daga Kano.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: