Connect with us

MAKALAR YAU

Abin Da Buhari Zai Koya A Tarihin Musulinci

Published

on

Wannan bayani ne ta fuskar ilimin halayyar jama’a a tarihin musulinci. Kamar yadda na taba fada a baya, ilimin halayyar jama’a (Sociology) ba yana fadin abin da ya kamata a yi bane tamkar a ilimin dabi’u (Ethics) a Falsafa, shi yana maganar yadda jama’a suke ne. Don haka aka bayyana cewa ita Falsafa tana magana akan abin da ake fatan ya faru (What should) amma shi ilimin halayyar jama’a yana magana akan abin da yake faruwa ne (What is).

Wannan shi ne abin da aka ce mu kula da shi a tarihi amma al’ummarmu take tafiya wani guri na daban. Duk abin da ya faru a tarihi ya riga ya faru sai dai mu yi izina da abin da ya faru din don mu gane daga inda muka fito kuma ina zamu dosa. Dalilin haka ya sa na duba tarihin fadi-tashin musulmi da tarihinsu domin Shugaba Muhammad Buhari da sauran shugabanni su sake izina a kai.

Sayyidi Umar ya fahimci cewa hanyar da zaka iya juya talakawan da kake mulka shi ne ka bayyana cewa rayuwarka irin tasu ce. Wani lokacin ma har ka takurawa kanka domin ka samu nasarar da talakawanka za su dinga girmamaka ba tare da ka samu matsalar mulki ba. Kowane talaka yana son ganin shugabansa bai banbanta da shi ba.

Tare da girman daular musulinci a zamanin Halifa Umar bn Khattab amma an tabbatar ya yi rayuwa irin ta talakawan zamaninsa. Bude Farisa ko Rum bai hana shi kwanciya kan tabarmar kaba ba. Kasancewar shari’ar musulinci tana hannunsa bai hana sanyawa a yi wa dansa haddi ba (kamar yadda aka rawaito). Har ta kai yana tauyewa kansa hakkoki domin ya zama na kusa da talakawa.

Wannan ta sanya talakawa suka dinga yi masa kallon dan cikinsu da ya zama wakilinsu, don haka ba su yi masa bore ba. Talaka ya yi kusa da mulki, mai kudi ya ci gaba da kasuwancinsa. Har sai da ya zama ana bayar da misalin zamaninsa a daya daga cikin manyan zamuna da aka samu adalci a “Khilafa-rashida”. Hakan ba ya nufin bai taba kuskure ba, waye ma’asumi bayan Manzon Allah (saw)?

Lokacin da Sayyidi Usman ya karbi mulki sai yan uwansa daga Banu Umayya suka kewaye shi. Sai mulkin ya koma hannun masu kudi. Masu kudi suka kara yin kudi kuma talaka ya koma talaucinsa. An rawaito cewa Sayyidi Usman ya taba bawa sirikinsa kyautar kudade masu yawa daga “Baitul Mali” wanda har sai da Abu Zarr Algifary ya tanka masa akan haka. Sanadiyar da ta sanya ya ajiye aikinsa kenan a gwamnatin.

Wannan ya janyo abin da masu “Sociology” suke kira da “Class Struggle” (rigimar bangare biyu) a tsakanin masu kudi da talakawa. Mafi yawan talakawa suka fara tsanar yan kadan daga masu kudi. Wadanda ake mulka suka dinga bi kusufa-kusufa don neman laifin Sayyidi Usman. An rawaito cewa har sai da takai mutanen Madina suna tankawa Sayyidi Usman irin abin da Sayyidi Umar ya yi amma ake ganin falala ce amma shi idan ya yi sai a ce bai dace ba!

Wannan shi ne babban abin da ya janyo aka fara yi wa Sayyidi Usman zanga-zanga. Mulkinsa ya cika da irin abin da masu Kimiyyar Siyasa (Political Science) suke kira da “nepotism” wato mulkin dangi. Yan kadan daga Banu Umayya suka dinga juya masu yawa daga sauran musulmi. Sayyidi Usman ba shi da hannu, an misalta shi da cewa mutum ne da bayan ya tsufa sosai (shekara 80+) kuma yana da sanyi sosai. Masu laifin sun hada da irin su Marwan bnl Hakam da Abdullahi bn Saad Ibn Abi Sarh.

Kada a manta, shi dama Sayyidi Usman mai kudi ne da ya saba rabon kudi da kuma kashe kudi. Shi kam Sayyidi Umar talaka ne da ya saba da rayuwar talauci da wahalhalun rayuwa. Kuma da yake masana ilimin halayyar dan Adam (Psychology) sun fadi cewa mutane suna auna na gaba da abin da na baya ya aikata ne, sai ya zama ana auna Sayyidi Umar talaka da dabi’un Sayyidi Usman mai kudi. Ka ko san babu yadda za’a yi a samu aiyuka iri daya daga mutane mabanbanta.

Kowa ya san cewa “Fitnat Usman” ita ta janyo duka matsalar da musulmi suka shiga daga baya. Daga  “Ma’arikat Siffen” zuwa “Mauki’at Jamal” har bullar “Nahrawan” da ma abin da ya kai ga “Karbala”. Masu falsafar tarihi duka za su iya hade maka abubuwan da ya faru. Kuma a takaice dai duka abin da ya janyo ba komai bane illa abin da masu “Sociology” suka kira “Class Struggle” wato rigima tsakanin talakan da yake ganin an danne shi da masu kudin da ake ganin su suka danne din, kamar yadda na fada a baya.

Ko me masu mulkin garinmu za su koya a wannan babban tarihi? Mutane suna zaton farin jinin Buhari yana da alaka da wani sirri da basu sani ba. Haka da ma mutane suke, duk abin da basu gane ba sai su hada shi da cewa “sirri” ne ko wani abu “mysterious” (mai ban mamaki) da suka kasa ganewa. Amma duka abin mai sauki ne idan muka kalle shi ta fuskar ilimin halayyar jama’a.

Buhari ya dade yana nunawa cewa shi talaka ne kamar mafi yawan yan Nijeriya. Hasalima har yana nuna musu cewa a wannan “class struggle” din yazo don ya yaki masu danniya ne (oppressors) don shi ma yana daga cikin wadanda aka danne (oppressed). Shekaru masu yawa yana nuna cewa shi mai gaskiya ne kuma yana bayan talaka, don rayuwa ma iri daya suke. Babu talakan da yake tsammanin Buhari yana da gidaje a Abuja ko yana da motoci sama da uku. Don haka yana ganin nasa ne ya samu.

Wannan shi ne abin da yasa talaka ya yarda da Buhari tare da ya kasa gane dalilin soyayyar tasa. Ya kara kudin mai amma talaka ya dauka don shi akai, abinci ya yi tsada shi ma talaka ya dauka ai maganin barayi ake, rayuwa ta kara wuya amma saboda imanin talaka ya dauka duk don da shi ake yi. Duk wannan bai damu talaka ba har sai da wani babban kuskure da Buhari ya fara yi ya bayyana.

Lokacin da aka ce an fara ganin baburin da Yusuf Buhari ya hau ya kai kimanin naira miliyan hamsin, sai talaka ya fara tunanin cewa Buhari ba nasa bane. Wadanda suke bin Aisha Buhari suna lissafa kudin jakarta da takalminta sun san yadda za su iya juya talaka ya dena son Buhari ba tare da ya gane ba. Lokacin da talaka yake kasa siyo kwanon shinkafa uku, a lokacin aka hango jakar matar Buhari ta “Ferragamo” ,”Gucci” da “Calbin Klein” ta dubunnan nairori.

Idan ka kalli yadda aka dinga murna saboda an cire Lawal Daura daga mukaminsa da kuma yadda ake ta so a saurari kukan da wani da ya zargi Abba Kyari da cinye masa kudi, hakan zai nuna maka cewa jama’a suna ganin Buhari mulkin dangi da abokai yake wanda na kira da “nepotism” a sama. Tare da cewa har yanzu suna son Buhari amma suna ganin mulkinsa bai yi ba tun da yana tare da masu hana su abin da suke fatan samu a mulkinsa. Wadanda aka kira “cabals” din da suke cin dunduniyarsa. Rashin ciresu kuwa zai janyo a tsani Buhari irin tsanar da ba’a taba yi wa wani shugaba ba.

Babbar matsalar ita ce shi mulki lalata mutum yake. Kamar yadda wani masanin falsafa yake fada “Power corrupts”. Don haka zai wuya Buhari ya saurari masu cewa ya canja salon mulkinsa musamman tun da akwai mutanen da yake gani suna sonsa da dalilin da su ma basu gane ba. Zai ci gaba da mulkinsa yadda ya saba kuma idan ya zarce ya dora a inda ya faro har sai kowane talaka ya tsane shi a kasar nan, ciki kuwa har da masu yi masa makauniyar soyayya a yanzu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: