A shafinmu na Al’adu, wanda za a fara wallafawa wannan satin, muna so mu rika kawo maku abin da ya shafi al’adu iri-iri. A wannan makon za mu fara muku da yadda kunya ta kasance a rayuwar Bahaushe a jiya, da kuma yadda abin ya sauya ta shiga wani hali na daban a yau, domin kuwa ta samu ‘yan sauye-sauye, sakamakon mu’amalar wasu da wasu bakin kabilu da suka shigo kasar Hausa, suka mamaye.
Manyan al’umma da suka fi tasiri a kan rayuwar Bahaushe su ne Larabawa da Turawa. Don haka za mu fara waiwaye ta kansu.
Larabawa
Larabawa da suka shigo kasar Hausa, sun kawo Addinin Musulunci, wanda ya fidda rayuwar Bahaushe daga duhun kai na Addinin Maguzanci zuwa haske na Addinin Musulunci. Don haka aƙidun Balarabiyar al’ada wacce ta dogara kacokan kan koyar alƙur’ani da sunnah ta yi tasiri a rayuwar Bahaushe. Akwai al’adun Bahaushe da aka watsar saboda sun saɓa wa ƙa’ida, akwai kuma waɗanda aka cigaba da runguma sabo da sun dace da ƙa’ida. Cikin waɗanda aka cigaba da rungumar “kunya” na ciki. Dalili kuwa yana cikin koyarwar Alƙur’ani da Hadisi kamar yadda ayoyi suka tabbatar da hakan a baya. Don haka mu’amalar Bahaushe da Balarabe kyawawan sauyi aka samu cikin rayuwar Hausa.
Addinin Musulunci shi ne addinin Bahaushe ya karɓa bayan fita daga duhun kai (Maguzanci) Musulunci ya yi tasiri sosai kan rayuwar Bahaushe wajen jaddada nasa bin umurni da hani na Allah (SWT) da kuma bin tafarki Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, (SAW). Kunya abu ne mai Muhimmanci da matsayi a Musulunci. Wannan ya tabbata ne cikin wasu ayoyin ƙur’ani da Hadisan Annabi Muhammad (SAW) kamar haka:
Allah madaukakin sarki ya ce
“Lalle wannan yana cutar da Annabi, to yana jin kunyarku alhali kuwa Allah ba ya jin kunya da gaskiya…” (kur’ani 33:53) (Fassara Gumi)
Haka kuma cikin alkur’ani mai girma, an kawo kissar Annabi Musa, wajen da taimaka wa ‘ya’yan Annabi Shu’aibu shayar da dabbobinsu. Saboda wannan taimakawar ne mahaifinsu ya umurce su, da su kirawo ya zo, zuwa gare shi. Allah (SWT) ya ce
“Sai ɗayansu ta je masa tana tafiya a kan jin kunya, ta ce “Ubana yana kiran ka, domin ya saka maka ijarar abin da ka shayar, saboda mu” ……… (ƙur’ani 28:25) (Fassarar Gumi)
Wadannan duk ayoyi ne da ke jaddada “kunya” cikin Alƙur’ani Mai Girma. Hakazalika Hadisan Manzon Allah ma, sun jaddada muhimmanci da matsayin ‘kunya’ a Addinin Musulunci kamar yadda cikin hadisi an ce:
“Daga Abu Sa’idul Khudri, Allah ya ƙara masa yarda yace “Manzon Allah (SAW) ya fi kowa jin kunya, mukan gane abin da ba ya so ne ta fuskar sa”.
Haku kuma wani ruwaya ta Bukhari an ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce
“kunya daga cikin imani ne shi kuma imani daga cikin aljannace” (Bukhari ne ya Ruwaito)
A wata ruwaya kuma an ce
“Manzon Allah (SAW) ya ce “kunya da imani an haɗa su wuri guda idan aka ɗauke ɗayan to shi ma ɗayan zai tafi”
(Muslim ne ya ruwaito)
An kuma ƙara faɗin Manzon Allah (SAW) yana cewa
“lallai kunya da imani aƙida ne na Musulmi”
(Minhajul Muslim)
Dukkanin wadannan ayoyin Alkur’ani da Haidisai jaddada matsayi da Muhimmancin kunya ne suke yi cikin Addinin Musulunci.
Turawa
Kamar yadda zuwan Balarabe kasar Hausa ya kawo tasiri ga rayuwar Bahaushe, haka zuwan turawa. Duk da cewa zuwan Bature ya kawo tasiri ga rayuwar Bahaushe ta samar da wasu kayayyakin more rayuwa da, da can baya bai san su ba, amma kuma sun kawo tarnaƙi ga wasu al’adun Hausawa, waɗanda daga cikin su akwai “Kunya”.