Daga Abubakar Abba,
Sakamakon wani sabon bincike da aka gudanar a fannin aikin noma a Nijeriya, an nuna cewa, akwai bukatar a hada karfi da karfe a tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa domin a bunkasa aikin noma a kasar.
Har ila yau, binciken ya kara da cewa, akwai bukatar daukar matakan da suka dace domin a kara bunkasa fannin noma a kasar nan.
A cewar binciken, shekaru da dama da suka shige, tsohon shugaban kasa kuma daya daga cikin jigogin da suka kafa kasar Amurka Thomas Jefferson, ya taba cewa, aikin noma shi ne ginshikin da muka sanya a gaba domin yana samar da arziki da kyakkyawar dabi’a da kuma jin dadi.
Allah ya albarkaci Nijeriya da wadatacciyar kasar noma da aka kiyasta ta kai fadin eka miliyan 91 da kuma kimanin kada-kada miliyan 8 sannan kuma ga dausayi mai kyawun gaske dake kaiwa har tsawon zagayowar shekara.
Kada-kada miliyan 18 da aka kiyasta, an raba ta gida biyu da ta din-din da kuma wadda ake yin kiwo, haka kuma babu tantama Nijeriya kasar noma ce, in ji binciken.
Sama da shekaru da suka shige, tun lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kanta, danyen mai ya janyo aikin noma ya yi kasa, inda hakan ya shafi abincin da ake nomawa a kasar, hakan kuma ya haifar da shigo da abinci daga kasashen ketare da janyo karancin abinci a kasar.
Harkar noma ba kawai ta shafi noma ba ne, harda kiwo musamman yadda ake gani ana yi a Arewacin Nijeriya.
Har ila yau, akwai bukatar kara mayar da hankali a kan kiwo baya ga kiwon shanu da noman kifi, akwai kuma bukatar yin kiwon aladu ta hanyar tsarin da a turance ake kira da “PorkMoney” wato samun kudi ta hanyar aladu.
Tsarin na pork an sanshi a fadin duniya, inda ya kai sama da kashi 40 na naman da ake ci.
A cewar masu binciken, yana dauke da sanadarin (protein) mai yawa da kuma sanadarin Bitamin dana minerals da amino acid wadanda sukkan wadannan sanadaran suna inganta lafiyar jikin dan adam.
Wasu daga cikin samfarin irin wannan naman, kamar wanda ake kira a turance tenderloin da loin chops da sirloin roast sunfi sanya lafiya ga jikin dan adam fiye da Kifi.
Wannan fannin na kasuwanci, tsari ne da yake sanya lafiya kuma hanya ce ta samun kudin shiga ga masu yin sana’ar.
Tuni ga wasu ‘yan Nijeriya da suka rungumi wannan sana’ar ta (PorkMoney) sun samar da wasu tsari ta hanyar ajiye Naira 250,000 tare da abokan cinikayyar su a karkashin jagorancin wani dan wasa kuma dan kasuwa dan kasar Ghana mai suna John Dumelo da Oke-Aro.
Har ila yau, za su fara kiwon aladu wadda za ta kasance mafi girma a Nahiyar Afrika don fara aikin a Nijeriya da kasar Ghana wadda a hankali sana’ar za ta bazu zuwa wasu kasashen da ke Afrika.