Bello Hamza" />

Abin Da Saraki Da Dogara Suka Tattauna Da Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wani taro da shugaban majakisar dattijai Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara a fadar shugaban kasa da safiyar ranar Laraba 27 ga watan Yuni 2018 inda suka tattauna halin da harkar tsaro ke ciki a jihar Filato tun bayan hare haren da tayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Shugaba majalisar dattija Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da shugaban kasa Buhari sun gudanar da tataunawar ne a sirrance. Sanarwar da jami’in watsa labarai na  shugaban majalisar wakilan ya raba wa manema labarai ta ce, shugabannin majalisar kasar ne suka nemi ganawa da shugaban kasar.

“A yau ni da shugaban majalisar dattijai Dakta Abubakar Bukola Saraki, mun yi taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari inda muka tattauna a kan rikicin daya auku a jihar Filato.

“Mun bukaci kiran taron ne don ji daga shugaban kasa abinda bangaren shugaban kasan keyi ada kuma matakan da suka dauka domin kawo karshen wannan mummunan lamarin dake faruwa a jihar Filato dama saurar sassan kasar nan gaba daya.

“A yau ni da shugaban majalisar dattijai Dakta Abubakar Bukola Saraki, mun yi taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari inda muka tattauna a kan rikicin daya auku a jihar Filato.

“Mun bukaci kiran taron ne don ji daga shugaban kasa abinda bangaren shugaban kasan keyi ada kuma matakan da suka dauka domin kawo karshen wannan mummunan lamarin dake faruwa a jihar Filato dama saurar sassan kasar nan gaba daya.

“Mun kuma amfani da wannan daman wajen ba shugaban kasar shawara akan hanyoyin daya kamata ya dauka don kawo karshen rikicin ya kuma kawo tabbatace zaman lafiya, kamar dai shawarar da zaman hadaddiya majalisar kasa tayi a cikin siri makwanni da suka wuce.

“Muna kuma kira ga dukkan bangarorin gwamnati dake da ruwa da tsaki dasu gaggauta bayar da agajin gaggauwa ga wurare da wadanda rikicin ya shafa.

“Majalisar wakilai tare da daukacin majalisar kasa, zata ci gaba da samar da dokokin daya kamata ga dukkan rundunonin tsaronmu, musamman a kana bin daya shafi samar da isassan kudade da kayan aiki don su samu karfin fuskanta da maganin dukkan matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta.

“Ina kuma sake kiran dana yi a baya na a sake yin garan bawul ga dukkan rundunonin tsaronmu don sun kasa shawo kan halin rashin tsaron da kasar nan ke funkanta.

“Ina kuma mai amfani da wannan dama wajen mika ta’aziyyata ga iyalan wadanda halin rashin tsaron nan ya rutsa dasu a jihohin Zamfara da Binuwai da Filato da Taraba da Adamawa da Kaduna da Nasarawa da Borno da kuma Yobe da sauran wurare daban daban, ina kuma kira ga ‘yan Nijeriya dasu akidar zaman lafiya don a samu cikakken ci gaba da bunkasar kasa.”

 

Exit mobile version